Gwamnati Ta Fadawa Kotu Yadda Emefiele Ya 'Shirga' Karya Domin Samun $6.2m
- Gwamnatin Najeriya ta zargi Godwin Emefiele da fakewa da sunan SGF wajen samun $6.3m gabanin zaben 2023
- Rotimi Oyedepo (SAN) ya yi kara a kotun tarayya a kan yadda CBN ya ba April 1616 Investment Ltd kwangiloli
- Ana zargin mata da surukin tsohon gwamnan CBN sun amfana da kwangilolin da aka bada daga 2018 zuwa 2020
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Gwamnatin tarayya ta zargi tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele da karya domin samun $6.23m.
A sababbin zargin da gwamnatin Najeriya take tuhumar Godwin Emefiele, The Nation ta ce akwai yin karya da nufin samun kudi.
Sauran zargin da Rotimi Oyedepo (SAN) ya jefi tsohon gwamnan da shi sun kunshi cin amana da karya kafin dakartar da shi daga CBN.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Godwin Emefiele ya yi amfani da sunan SGF?
A cewar Rotimi Oyedepo (SAN), Mista Emefiele ya hada kai da wani Odoh Eric Ocheme, aka karbi kudi da sunan sakataren gwamnati.
Odoh Ocheme wanda ake zargin sun samu miliyoyin daloli da sunan sakataren gwamnatin tarayya ya tsere, yanzu haka ana neman sa.
Badakalar kwangilolin Emefiele a CBN
Lauyan da ya shigar da kara, ya ce wanda ake tuhuma ya bada kwangilolin miliyoyi ga mai dakinsa Omoile Margaret da kuma surukinsa.
Gwamnatin tarayya tana zargin Omoile Macombo wanda kamfaninsu ya samu kwangilar CBN, ‘danuwan matar tsohon gwamna ne.
...karyar Emefiele da sunan masu sa idon zabe
Laifin da ake jifan Emefiele bai tsaya nan ba, ana tunanin ya yi amfani da takardar karya a Junairun 2023 da sunan masu sa idon zabe.
Bloomberg ta ce takarda mai lamba SGF.43/L.01/201 ba daga wajen jami’an ketare da suka zo lura da zaben 2023 da aka yi a ta fito ba.
Lauyan Emefiele ya karyata zargi
A Nuwamban 2023 aka zargi Emefiele da amfani da matsayinsa wajen ba kamfanin Sa’adatu Ramallan Yaro kwangiloli na N1.21bn.
Da aka je kotu, tsohon gwamnan na bankin CBN ya karyata duk zargin da ake yi masa ta bakin lauyansa, Matthew Burkaa (SAN).
Lauyan ya tabbatar da wannan ga kotun tarayyar da ke zama a Abuja kuma Alkali Hamza Muazu ya sasauta belin domin ya iya yawo.
Asali: Legit.ng