Tsohon Gwamnan CBN Ya Faɗi Gaskiya Kan Tuhume-Tuhume 20 da Ake Masa a Gaban Kotu
- Gwamnatin tarayya ta hannun EFCC ta ƙara gurfanar da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, a gaban kotu kan tuhume-tuhume 20
- A zaman yau Jumu'a a Abuja, Emefiele ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ɓangaren masu ƙara suka shigar a kansa
- Sai dai bayan muhawara kan batun lafiyar tsohon gwamnan, kotun ta ɗage zama zuwa ranakun 12 da 13 ga watan Fabrairu, 2024
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, ya musanta dukkan tuhume-tuhume 20 da aka shigar kansa a gaban kotu.
Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta ƙara yawan tuhume-tuhumen da take wa Emefiele, ta miƙa wa Kotu.
Sai dai yayin da aka sake gurfanar da shi a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Maitama, Abuja ranar Jumu'a, 19 ga watan Janairu, Emefiele ya musanta tuhume-tuhumen gaba ɗaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar The Nation ta tattaro, a halin yanzu babbar kotun ta sake ɗage sauraron shari'ar zuwa ranakun 12 da 13 ga watan Fabrairu, 2024.
Yadda zaman kotun ya gudana
Yayin zaman shari'ar, tawagar lauyan wanda ake kara sun roƙi kotu ta sahale wa Emefiele ya ci gaba da zama cikin belin da kotu ta ba shi a kwanakin baya.
Haka nan kuma lauyan masu ƙara bai yi musu kan wannan roko ba, inda ya ƙara da cewa suna son ya riƙa halartar zaman shari'ar cikin ƙoshin lafiya, rahoton The Cable.
Daga nan ne alkalin kotun, mai shari'a Hamza Muazu, ya aminta da sharuɗɗan belin da aka bai wa tsohon gwamnan CBN, Emefiele.
Kotun koli ta yu hukunci a shari'ar zaben Nasarawa
A wani rahoton kun ji cewa Daga karshe, Kotun Ƙolin Najeriya ta raba gardama kan taƙaddamar zaben gwamnan jihar Nasarawa da aka yi a watan Maris, 2023
Kwamitin alkalan kotun ƙarƙashin mai shari'a Kudirat ta kori ƙarar da ɗan takarar PDP ya ɗaukaka bisa hujjar rashin cancanta.
Asali: Legit.ng