Sufeto-Janar Na Yan Sanda Ya Dauki Muhimmin Mataki 1 Don Kawo Karshen Rashin Tsaro a Abuja

Sufeto-Janar Na Yan Sanda Ya Dauki Muhimmin Mataki 1 Don Kawo Karshen Rashin Tsaro a Abuja

  • Sufeto-Janar na ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya shoirya ƙaddamar da runduna ta musamman domin magance matsalar rashin tsaro a Abuja
  • Rundunar wacce za a ƙaddamar za a tura jami'anta zuwa dukkan ƙananan hukumomin da ke babban birnin tarayya Abuja
  • Rundunar za ta ƙunshi ƙwararrun jami'ai na musamman waɗands suka samu horo yayin da za a ba su kayan aiki na zamani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sufeto-Janar na ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, na shirin ƙaddamar da wata runduna ta musamman (SIS), domin daƙile ayyukan masu garkuwa da mutane a wasu sassan babban birnin tarayya Abuja.

Ya ce rundunar ta musamman idan aka kaddamar da ita, za a tura jami'anta ne zuwa dukkan ƙananan hukumomin da ke babban birnin tarayya Abuja, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun tafka sabuwar ta'asa cikin dare a jihar Neja

IGP zai kaddamar da sabuwar runduna
IGP Egbetokun zai kaddamar da sabuwar runduna don dakile rashin tsaro a Abuja Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

A cikin kwanakin dai ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane tare da kashe wasu mazauna yankin Bwari na babban birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

IGP ya ce rundunar ta ƙunshi ƙwararrun jami’an da suka samu horo na musamman da suka shirya magance matsalar sace-sacen mutane, rahoton Radio Nigeria ya tabbatar.

Rundunar da za a tura za ta ƙunshi jami’ai na musamman, jirage masu saukar ungulu, jirage marasa matuƙa, motoci na musamman, da K9, da dai sauransu.

Wike ya gana da masu ruwa da tsaki a Abuja

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya shiga ganawar gaggawa da masu ruwa da tsaki a babban birnin tarayya Abuja.

Wike ya na gana ne da manyan jami'an tsaron birnin Abuja da masu sarautar gargajiya da kuma masu riƙe da hukumar FCTA, kan matsalar rashin tsaron da ta dabaibaye birnin na Abuja.

Kara karanta wannan

Atiku ya bayyana abin da ya hana kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan, ya fadi mafita

Tinubu Ya Gana da Hafsoshin Tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan, a fadarsa da ke Aso Rock Villa.

Shugaban ƙasar ya gayyato hafsoshin tsaron ne kan matsalar tsaro wacce ta addabi ƙasar nan, da ake ci gaba da fama da ita a sassa daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng