Abin Bakin Ciki Yayin Da Sojan Najeriya Ya Bindige Kansa, Ya Mutu Cikin Bariki, Bayanai Sun Fito

Abin Bakin Ciki Yayin Da Sojan Najeriya Ya Bindige Kansa, Ya Mutu Cikin Bariki, Bayanai Sun Fito

  • Wani jami'in sojan Najeriya, Boyi Thankgod, ya bindige kansa a kai kuma ya mutu yayin da ya ke jira a tura shi aiki
  • Lamarin, kamar yadda aka rahoto ya faru ne a Barikin Alamala a ranar Litinin yayin da ya ke bakin aiki a ranar Tunawa da Dakarun Sojoji
  • Wata majiya daga barikin ta tabbatar da lamarin, ta kara da cewa yan sandan sojoji sun fara bincike a kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Jihar Ogun - An rahoto cewa wani jami'in sojan Najeriya Boyi Thankgod, ya dauki ransa a Barikin Alamala da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

A cewar Daily Trust, jami'in sojan Najeriyan ya bindige kansa a kai lokacin da ya ke bakin aiki a ranar Tunawa da Sojojin da suka rasu.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana dalilin da ya sanya jami'in sojanta ya bindige kansa

Sojan Najeriya ya kashe kansa a Ogun
Jami'i sojan Najeriya ya dauki ransa a bariki a Ogun. Hoto: Rundunar Sojojin Najeriya
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoton, an tarar da gawar sojan cikin mummunan yanayi da raunin harsashin a kansa.

Yadda soja ya bindige kansa ya dauki ransa a Ogun

A cewar wata majiya a barikin, lamarin ya faru, kuma ya faru ne a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu.

Majiyar ta kara da cewa an fara bincike kan abin da ya kai sojan ga aikata wannan lamari mai tada hankali.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Da gaske abin ya faru. Tun jiya, yan sandan sojoji sun fara bincike... dukkan sojoji na wurin a lokacin da abin ya faru, an tsare su, an kuma bukaci su bada bayanai da wasu abubuwa da aka saba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164