Innalillahi: Fitacciyar Ma'aikaciya da Ake Ƙauna a Abuja Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, Bidiyo Ya Bayyana

Innalillahi: Fitacciyar Ma'aikaciya da Ake Ƙauna a Abuja Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, Bidiyo Ya Bayyana

  • Gidan radiyon Naija Info FM ya tabbatar da mutuwar ɗaya daga ciki ma'aikatan da tauraruwarsu ke haskawa, Deborah Ohamara
  • Kafar watsa labaran wadda ke aiki a birnin tarayya Abuja ta bayyana haka ne a wani gajeren saƙo da suka wallafa a manhajar X ranar Talata
  • Rahotanni sun bayyana cewa ma’aikaciyar gidan rediyon ta rasu ne sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da ita a hanyar filin jirgin Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT Abuja - Deborah Ohamara, fitacciyar ma’aikaciyar gidan rediyon Najeriya Info FM wacce aka fi sani da Naija Info FM 95.1 a Abuja ta riga mu gidan gaskiya.

Mai watsa shirye-shiryen ta rasa rayuwarta ne a wani haɗarin mota da ya rutsa da ita a titin filin jirgin saman Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ma'aikaciyar FM ta mutu a Abuja.
Wata Fitacciyar Ma'aikaciya a Abuja Ta Kwanta Dama, Bidiyo Ya Bayyana Hoto: @NigeriainfoAbj
Asali: Twitter

A rahoton da ta wallafa ranar Talata, 16 ga watan Janairu, 2024, ta saki bidiyon da ya tabbatar da faruwar mummunan lamarin.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya ki amsa gayyatar hukumar kula da da’ar ma’aikata

Daga faifan bidiyon da aka watsa, hadarin ya faru ne lokacin da wata babbar mota mai dauke da yashi ta yi karo da motar Deborah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wacece Deborah Ohamara?

An fi kiranta da sunan muryar zinare ta Naija Info, Abuja, saboda shirin da take jagoranta a gidan radiyon.

Haifaffiyar jihar Kuros Riba, Deborah, wadda masu saurarenta ke kiranta da Derbie, ta fara aikin jarida ne a gidan rediyon Kuros Riba (CRBC TV).

Haka nan kuma ta yi aiki a matsayin mai gabatarwa a tashar FM 105.5 Paradise FM da ke Kalaba.

Nigeria Info FM sun tabbatar da wannan rashi

Da take mayar da martani, Nigeria Info FM ta tabbatar da mutuwar Debbie a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, 15 ga watan Janairu.

Kafar yada labaran ta bayyana marigayyar a matsayin "wata mai basira kuma mai yada labaran da ake ƙauna", tare da sanar da cewa an bude rajistar ta'aziyya.

Kara karanta wannan

Ana ci gaba da kuka kan sace 'yan mata a Abuja, 'yan bindiga sun kuma sace wasu 45 a Benue

"Muna jimamin sanar da rasuwar Deborah Ohamara (Debbie), haziƙa kuma yar jarida da ake ƙauna da ke tare da Najeriya Info Abuja."

Mutane sun mutu a harin jihar Zamfara

A wani rahoton kuma Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai mummunan hari kauyen Magizawa da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Zamfara.

Mazauna yankin sun tabbatar da cewa maharan sun sace mutane 50 ciki harda mata 36 kana sun kashe rayuka 3.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262