Mai Kwacen Waya da Mota Ta Buge a Kano Ya Kwanta Dama
- Hukumar yan sandan jihar Kano ta yi karin bayani kan halin da ake ciki game da matashin da mota ta buge yayin da ya ke kwacen waya a jihar
- Kakakin yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce matashin ya riga mu gidan gaskiya bayan karyewa da kashin bayansa ya yi sakamakon hatsarin
- Tun a ranar Lahadi, 14 ga watan Janairu ne al'amarin ya afku inda ya mutu a yau Talata, bayan kwanaki biyu a asibiti
Jihar Kano - Rundunar yan sandan jihar Kano ta sanar da labarin mutuwar mutumin nan da mota ta buge bayan ya yi wa wata mata kwacen wayarta.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, kakakin rundunar yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da cewar mutumin ya mutu ne a asibitin Murtala da ke garin Kano.
Yadda kashin bayan barawon waya ya karye a Kano, Yan sanda
Tun farko dai Kiyawa ya sanar da halin da matashin ke ciki, wanda alhakin baiwar Allah ya kama da shi tare da zama silar kamuwarsa da lalurar karyewar kanshi baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kiyawa ya bayar da cigiyar ne yayin zantawa da manema labarai, yana mai cewa mata matashin yana karkashin kulawar likitoci cikin wani mawuyacin hali.
A cewar Kiyawa, har kawo lokacin sun kasa samun wata shaida da zata bayyana sunan matashin ko kuma daga inda ya fito.
Yadda Lamarin ya faru
A ranar Lahadi ne rundunar yan sandan Kano ta ce ta samu kiran gaggawa daga yankin Unguwar Zoo Road, cewa ga wani matashi mota ta take shi.
Hakan ya biyo bayan yadda matashin ya kwacewa wata mata wayarta, ta hanyar zare mata makamin Danbuda.
A cewar kakakin rundunar yan sandan, bayan ya kwace wayar ne ba tare da duba titi ba kawai ya afka, kuma daga wani Mai Mota yayi awon gaba da Shi.
"Bayan jami'an mu sun zo tare da kai Shi asibitin Murtala, likitoci Sun tabbatar mana da cewa kan sa ya fashe kuma ya gamu da lalurar karyewar kashin baya, (Spinal Code)."
Yanzu haka dai matashin na can cikin wani hali na rai kwakwai mutu kwakwai.
NDLEA ta kama dalibai a Kano
A wani labarin, mun ji cewa hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a jihar Kano ta yi karin haske kan cewa dalibai shida cikin 10 da ke jihar suna shan miyagun kwayoyi.
Babban Sufeton NDLEA na jihar, Jibril Ibrahim, ya bayyana cewa adadin masu shan miyagun kwayoyi a tsakanin dalibai ya yi yawa kuma ana iya cewa ya haura kashi 50% cikin dari.
Asali: Legit.ng