GEJ: Innaillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Tsohon Shugaban Ƙasa Ya Yi Babban Rashi a Najeriya

GEJ: Innaillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Tsohon Shugaban Ƙasa Ya Yi Babban Rashi a Najeriya

  • Allah ya yi wa yayar tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Jonathan, rasuwa bayan fama da ƴar gejeruwar jinya a Bayelsa
  • Madam Obebhatein Jonathan ta rasu ne tana da shekaru 70 a duniya ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu, 2023
  • A wata sanarwa da ofishin midiya na Jonathan ya fitar, ta ce za a yi jana'iza ranar Talata 16 ga watan da muke ciki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bayelsa - Tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya yi babban rashi yayin da yayarsa, Madam Obebhatein Jonathan, ta riga mu gidan gaskiya.

Ƴar uwar tsohon shugaban ƙasar ta rasu ne ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu, 2024 a babban asibitin tarayya FMC da ke Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Mutane sama da 20 sun mutu yayin da jirage biyu suka yi mummunan hatsari a jihar PDP

Dakta Goodluck Jonathan.
Tsohon Shugaban Kasa Ya Yi Babban Rashi, Allah Ya Yi Wa Yayarsa Rasuwa Hoto: Dr. Goodluck Jonathan
Asali: Facebook

Marigayya Madam Obebhatein ta mutu ne bayan fama ta jinya ta ƙanƙanin lokaci tana da shekaru 70 a duniya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ofishin midiya na tsohon shugaban ƙasa Jonathan ya tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ya fitar yau Alhamis.

Sanarwan ta bayyana cewa marigayya Obebhatein wacce aka fi sani da Amissi ta kasance tsohuwar malamar makaranta, ƴar kasuwa kuma uwa ta gari da kowane ɗa ke fata.

A cewar sanarwan, marigayyan ta yi rayuwa mai ban sha'awa mai cike da sadaukarwa ga Allah da kuma yi wa al'umma hidima.

Ta kasance mai bin addinin Kirista kuma ba ta wasa da ibada, mace tagari kuma abin koyi ga mutane da yawa a ciki da wajen al'ummar yankinta, Dailypost ta tattaro.

Yaushe za a yi jana'izar marigayya?

Sanarwar ta kuma nuna cewa an shirya jana’izar matar ne a ranar Talata 16 ga Fabrairu, 2024 kuma ta jaddada cewa za a sanar da cikakken bayani nan ba da daɗewa ba.

Kara karanta wannan

Matashi ya yi nadama bayan sayar da gidansa don burge budurwarsa, ta yi masa abin da bai yi zato ba

Madam Obebhatein Jonathan ta rasu ta bar ‘ya’ya uku da ‘yan’uwa da dama ciki har da mai girma Dokta Goodluck Ebele Jonathan, da mahaifiyarta Mama Eunice Afeni-Jonathan.

An kara kama masu hannu a kashe-kashen Filato

A wani rahoton kuma Dakarun yan sanda sun kara kama waɗanda ake zargi da hannu a kisan bayin Allah sama da 150 a jihar Filato.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda, Muyiwa Adejobi, ya ce an kama ƙarin mutum 3 masu safarar bindigu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262