Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Tsohon Ministan Da Ake Zargi Da Karkatar Da $6bn
- Babbar kotun Abuja ta bada belin tsohon ministan wutar lantarki, Olu Agunloye, kan kuɗi Naira miliyan 50 ranar Alhamis
- Hukumar EFCC ta gurfanar da Mista Agunloye gaban ƙuliya ne kan zargin damfara a kwangilar tashar wutar mambila
- Alkalin kotun ya amince da belin amma ya karɓe farfo ɗin tsohon ministan kuuma ya gindaya masa sharuɗɗa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babbar kotun birnin tarayya Abuja ta ba da belin tsohon ministan wutar lantarki da ƙarafa, Olu Agunloye, kan kudi Naira miliyan 50.
Alkalin kotun, mai shari'a Jude Onwuegbuzie, shi ne ya amince da bada belin tsohon ministan a zaman ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu, 2024, Channels tv ta ruwaito.
An gurfanar da Agunloye ne a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume bakwai da suka shafi bada kwangilar damfara da kuma almundahana a hukumance, ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, na binciken Agunloye kan kwangilar samar da wutar lantarki ta Mambilla ta dala biliyan 6.
Bayan gurfanar da shi, Alkalin kotun ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a gidan gyaran halin Kuje har zuwa lokacin da za a saurara tare da yanke hukunci kan neman beli.
Yadda zaman kotu ya gudana
Da yake gabatar da bukatar, Lauyan tsohon ministan, Adeola Adedipe, ya roki kotu da ta bayar da belin wanda yake karewa bisa la'akari da sanayya ko kuma sassauci.
Ya ce Argunloye ba mutum ne mai ƙafar yawo ba kuma masu gabatar da kara sun gurfanar da shi ne sakamakon rashin fahimta da rashin sani.
Nesa ta zo kusa: Kotun koli ta sanya ranar yanke hukuncin kan zaben gwamnan Kano, Bauchi da wasu jihohi 5
Adedipe ya kuma roki kotu da kada ta bada umarnin a yi amfani da ma’aikacin gwamnati a matsayin wanda zai tsayawa wanda yake karewa yayin bada belin.
Sai dai lauyan masu gabatar da ƙara ya nuna rashin aminta da buƙatar bada belin tsohon ministan, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Hukuncin da kotu ta yanke
Da yake yanke hukuncin kan buƙatar belin, mai shari’a Onwuegbuzie ya ce ra'ayin kotun ya karkata ga bayar da belin wanda ake tuhuma.
Ya bayar da belin wanda ake tuhuma kan Naira miliyan 50, sannan ya umarce shi da ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa.
Alkalin ya kuma umarci tsohon ministan ya miƙa fasfo ɗinsa ga kotun kuma dole ya halarci dukkan zaman da za a yi a shari'ar. Daga nan ya ɗage zaman zuwa 12 ga watan Fabrairu.
Gwamnonin APC sun sa labule a Abuja
A wani rahoton na daban Ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC na ganawar sirri yanzu haka a masaukin gwamnan jihar Imo da ke Asokoro a birnin tarayya Abuja
An gano cewa shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ne ke jagorantar zaman yau Alhamis.
Asali: Legit.ng