Dattawan Kano Sun Magantu Kan Samamen EFCC a Ofishin Dangote, Sun Fadi Abin da Hakan Ke Nufi

Dattawan Kano Sun Magantu Kan Samamen EFCC a Ofishin Dangote, Sun Fadi Abin da Hakan Ke Nufi

  • Kungiyar Dattawan Arewa ta yi Allah wadai da samame da hukumar EFCC ta kai a ofishin kamfanin Dangote
  • Kungiyar reshen jihar Kano ta ce wannan ba karamar illa ba ce ga tattalin arzikin Najeriya baki daya
  • Hakan ya biyo bayan samamen da hukumar EFCC ta kai a ofishin a ranar 4 ga watan Janairu a Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kungiyar Dattawan Arewa reshen jihar Kano ta fusata da samamen da EFCC ta kai ofishin kamfanin Dangote a Legas.

Kungiyar ta ce wannan samame zai kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya gaba daya, cewar Leadership.

Dattawan Kano sun magantu kan samamen da EFCC suka kai ofishin Dangote
Dattawan Kano sun yi martani kan samamen EFCC a ofishin Dangote. Hoto: @AlikoDangote, @efccnigeria.
Asali: Twitter

Martanin kungiyar kan samamen EFCC a ofishin Dangote

Kara karanta wannan

Kano Pillars ta durkusa gaban Hukumar NFFL, ta nemi taimako kan dalili 1, bayanai sun fito

Bello Sani Galadanci, sakataren yada labaran kungiyar shi ya tabbatar da haka ga manema labarai a Kano a jiya Laraba 10 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Galadanci ya ce mutanen Kano ba su ji dadin haka ba saboda barazana ce ga tattalin arzikin Najeriya da kuma tsorata masu zuba hannun jari.

Sanarwar ta ce:

"Kungiyar Dattawan Arewa da jama'ar jihar Kano sun kadu da samame da EFCC ta kai a ofishin kamfanin Dangote.
"Wannan samame barazana ce ga tattalin arzikin Najeriya da kuma tsorata masu son zuba hannun jari a kasar da kawo cikas ga ci gaba.
"Tabbas hakan zai kara matsin tattalin arziki da ake ciki da hana masu son zuba hannun jari a nan gaba."

Mene dalilin kai samamen EFCC ofishin Dangote?

Idan ba mantaba, Hausa Legit ta ruwaito cewa a ranar 4 ga watan Janairu hukumar EFCC ta dira ofishin kamfanin Dangote da ke jihar Legas.

Kara karanta wannan

Tashin hankali bayan 'yan daba sun farmaki Sanatan Arewa a Gidan Gwamnati, an kama mutum 6

Wannan samame ya biyo bayan binciken da ake yi kan wasu kamfanoni 52 da sha'anin canjin kudade ya shafa cikin shekaru 10.

Kafin kai samamen, Kamfanin Dangote ya nemi bahasin me yasa ake bukatar takardun amma a duk a banza, Premium Times ta tattaro.

EFCC ta dira a babban ofishin kamfanin Dangote

A wani labarin, Hukumar EFCC ta kai samame babban ofishin kamfanin Dangote da ke jihar Legas kan wani bincike da ta ke yi.

An tabbatar da cewa EFCC ta na binciken wasu kamfanoni ne da zargin badakala a lamarin canjin kudaden Najeriya.

Mutane da dama da masu ruwa da tsaki sun soki matakin da cewa zai dakile masu zuba hannun jari shigowa kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel