Badaƙala: EFCC Ta Tatsi Muhimman Bayanai, Ta Ɗauki Mataki Kan Ministar da Tinubu Ya Dakatar

Badaƙala: EFCC Ta Tatsi Muhimman Bayanai, Ta Ɗauki Mataki Kan Ministar da Tinubu Ya Dakatar

  • Bayan shafe tsawon awanni tana shan tambayoyi, EFCC ta bada belin Betta Edu, dakatacciyar ministar jin ƙai da yaƙi da talauci
  • Misis Edu ta mika kanta ga EFCC ranar Talata da safe kuma tun lokacin har zuwa dare tana hedkwatar hukumar kafin daga bisani a bada belinta
  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da Betta Edu ne bayan zarginta da hannu a badakalar tura wasu kuɗi asusun kai da kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati (EFCC) ta bayar da belin dakatacciyar ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Betta Edu.

EFCC ta bada belin Edu ne bayan titsiye ta da tambayoyi na tsawon sa'o'i kan zargin ta bada umarnin tura kuɗi N585m zuwa asusun kai da kai na wani ma'aikaci.

Kara karanta wannan

Babban Labari: Hukumar EFCC Ta Karbe Fasfon Betta Edu da Sadiya Umar-Farouq

EFCC ta bada belin Betta Edu.
EFCC ta bada belin dakatacciyar ministar harkokin jin kai, Betta Edu Hoto: EFCC, Betta Edu
Asali: Twitter

A ranar Litinin ne Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya dakatar da Misis Edu daga ofis sannan ya umarci EFCC ta gudanar da bincike kan badakalar da ake zargin da hannunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ba tare da ɓata lokaci ba hukumar EFCC ta aike da saƙon gayyata ga Edu, inda ta umarci ta kai kanta hedkwatar hukumar da ke Abuja ranar Talata.

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa Betta Edu ta amsa gayyatar da aka yi mata, ta kai kanta ofishin EFCC da safiyar Talata.

Tun da ta isa hedkwatar EFCC, jami'an hukumar suka fara mata tambayoyi kan badaƙalar da ta auku a ma'aikatarta har zuwa dare lokacin da aka bada belinta.

A rahoton da Channels tv ta tattaro, hukumar yaƙi da rashawa ta kwace fasfon tafiye-tafiya na Betta Edu kafin daga bisani su ba ta damar tafiya gida.

Kara karanta wannan

Badakalar N438m: Minista ya magantu bayan Tinubu ya kira shi zuwa Villa, bayanai sun fito

EFCC ta saki Betta Edu a beli

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatarwa da wakilin jaridar ranar Laraba cewa an bayar da belin Misis Edu a ranar Talata.

Amma Mista Oyewale, ya kaucewa yin tsokaci da ƙarin bayani kan ƙa'idoji da kuma sharuddan da ke kunshe a belin da aka bai wa dakatacciyar ministar.

A kalamansa, kakakin EFCC ya ce:

“An bayar da belinta a daren jiya Talata. Ina mai ƙara tabbatar muku da cewa har yanzu ana ci gaba da bincike."

Da aka matsa masa lamba ya yi tsokaci kan sharuddan belin da sakamakon zaman tambayoyin da aka yi a ranar Talata, Mista Oyewale ya ce, “Ba zan iya yin karin bayani kan batun ba."

Enitan ya maye gurbin Betta Edu

A wani rahoton kuma Abel Olumuyiwa Enitan ya karɓi ragamar jagorancin ma'aikatar jin ƙai da yaƙi da talauci bayan dakatar da Betta Edu.

Babban sakataren ma'aikatar ya maye gurbin Edu ne bisa umarnin shugaban ƙasa, Bola Tinubu, wanda ya dakatar da ministar ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262