Bayan Kama 8, Asirin Masu Hannu a Kisan Bayin Allah Sama da 150 Ya Ƙara Tonuwa a Arewa
- Dakarun yan sanda sun kara kama waɗanda ake zargi da hannu a kisan bayin Allah sama da 150 a jihar Filato
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda, Muyiwa Adejobi, ya ce an kama ƙarin mutum 3 masu safarar bindigu
- A ranar 24 ga watan Disamba, 2023 wasu tsageru suka kai farmaki kauyuka sama da 20 a kananan hukumomi 3 a Filato
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Plateau - Rundunar ƴan sandan Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun kama ƙarin mutum uku da ake zargin suna da hannu a kashe-kashen da ya faru a jihar Filato.
Muyiwa Adejobi, kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya (NPF), ya ce an kama ƙarin waɗanda zargi da hannu a hare-haren da aka kai wasu kauyukan jihar da ke Arewa ta Tsakiya.
Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa Adejobi ya bayyana haka ne yayin zantawa da yan jarida a birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
The Cable ta ce wannan ci gaban na zuwa ne kwanaki 5 kaɗai bayan rundunar ƴan sandan jihar Filato ta sanar da kama mutum 8 da zargin hannu a kashe-kashe na jajibirin kirsimeti.
Yadda aka kashe rayuka sama da 150
A ranar 24 ga Disamba, 2023, wasu ‘yan bindiga suka kai hare-hare masu muni kan kauyukan kananan hukumomin Barkin Ladi, Mangu, da Bokkos, inda suka kashe bayin Allah sama da 150.
Mutane da dama ne suka gudu suka bar matsugunansu bayan ƴan bindigan sun sake kaddamar da hari a wani kauyen na daban ranar 30 ga watan Disamba.
An kama karin masu hannu a kisan
Adejobi ya ƙara da bayanin cewa ƙarin mutane 3 da aka kama a yanzu, mambobin tawagar masu safarar bindigu ne, ana zargin suna da hannu a kitsa kai hare-haren.
Ya ce an kama mutanen ne bayan umarnin babban sufeton ‘yan sandan, Kayode Egbetokum, na tabbatar da cafke duk masu hannu a aikata ɗanyen aikin.
Ya ce an kwato motar Golf mai launin toka, AK-47 guda daya, bindigar AK-49 daya, harsasai 1,000, da kuma magazine biyar daga hannun wadanda ake zargin.
Kakakin rundunar ya kara da cewa ‘yan sanda na kokarin ganin an cafke duk wadanda ke da hannu a harin, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
Haɗarin jirage ya laƙume rayuka a Ribas
A wani rahoton kuma wasu jiragen ruwa guda biyu sun gamu da mummunan hatsari a yankin ƙaramar hukumar Andoni ta jihar Ribas jiya Talata.
Shugaban ƙaramar hukumar Andoni ya ce akalla mutane 20 suka mutu a haɗarin, ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwa.
Asali: Legit.ng