Betta Edu: EFCC Ta Tsitsiye Shugabannin Bankuna 3 Kan Badakalar N44bn, Bayanai Sun Fito

Betta Edu: EFCC Ta Tsitsiye Shugabannin Bankuna 3 Kan Badakalar N44bn, Bayanai Sun Fito

  • Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC) ta fara bincikar shugabannin bankunan Zenith, Providus da Jaiz
  • Hukumar na yi musu tambayoyi ne kan badaƙalar N44bn da aka bankaɗo a ma'aikatar jin ƙai da yaƙi da talauci
  • Hakan dai na zuwa ne bayan hukumar ta fara bincike kan Betta Edu da Halima Shehu waɗanda Shugaba Tinubu ya dakatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati (EFCC) ta titsiye shugabanni da manyan daraktocin bankunan Zenith, Providus, da Jaiz.

Hukumar tana yi wa jami'an tambayoyi ne kan badaƙalar sama da N44bn da aka bankaɗo a ma’aikatar jin ƙa da yaƙi da talauci.

EFCC ta fara bincikar bankuna uku
EFCC ta fara bincikar bankuna uku kan badakalar N44bn Hoto: @Edu_betta, @EFCC
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta rahoto cewa har ya zuwa ƙarfe 4:55 na yammacin ranar Talata, hukumar na yi musu tambayoyi a hedikwatarta dake Jabi a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Badakalar N438m: Minista ya magantu bayan Tinubu ya kira shi zuwa Villa, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministar jin ƙai Betta Edu da aka dakatar a halin yanzu tana tsare kuma tana fuskantar tuhuma daga hukumar EFCC kan badaƙalar N585m.

Meyasa EFCC ke binciken bankunan?

Wani majiya daga EFCC wanda ya tabbatar da lamarin ya bayyana cewa shugabannin na bankunan Zenith, Providus, da Jaiz ana yi musu tambayoyi kan badaƙalar N44.5bn da aka bankaɗo a ma’aikatar da ta shafi Betta Edu da Halima Shehu.

Majiyar ya ci gaba da cewa:

"A yanzu haka shugabannin bankunan Zenith, Providus, Jaiz suna amsa tambayoyi daga wajen masu yin binciken mu a hedikwata.
"An gayyace su kuma ana ci gaba da bincike kan su kan badaƙalar N44bn da aka bankaɗo da kuma N585m da suka haɗa da Halima Shehu da Betta Edu.
"Ministan da aka dakatar da shugabar hukumar NSIPA, duk sun yi sabon bayani a lokacin da ake yi musu tambayoyi, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike."

Kara karanta wannan

Badaƙalar N37bn: Jami'an EFCC sun titsiye tsohuwar ministar Buhari, sun tashi muhimman bayanai

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da Edu ne a ranar Litinin, bisa zargin badakalar kuɗi har N585m.

Betta Edu Ta Shiga Hannun EFCC

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministar jin ƙai da yaƙi da talauci, Dr Betta Edu, wacce Shugaba Tinubu ya dakatar ta shiga hannun EFCC.

Betta Edu ta shiga hannun hukumar ne domin amsa tambayoyi kan badaƙalar N548m da ake zarginta da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng