Badakalar N438m: Minista Ya Magantu Bayan Tinubu Ya Kira Shi Zuwa Villa, Bayanai Sun Fito
- Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, wanda aka gayyace shi zuwa fadar shugaban kasa sa’o’i 24 kacal bayan dakatar da Betta Edu, ya yi tsokaci
- Yayin da yake barin fadar shugaban kasa, ƴan jarida sun tuntubi ministan domin tattaunawa amma ya ce komai daidai
- Tunji-Ojo dai ana zarginsa ne da karɓar N438m kuɗin wata kwangila na kamfanin da ya kafa amma ya ce ya ajiye mukamin daraktansa tun da ya shiga siyasa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu, a ranar Talata, 9 ga watan Janairu, ya gayyaci ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, zuwa fadar shugaban ƙasa ta Villa, kan alaƙarsa da Betta Edu.
Hakan dai na zuwa ne sa'o'i 24 da dakatar da takwararsa ta ma'aikatar jin ƙai da yaƙi da talauci Dr Betta Edu.
An gayyaci Tunji-Ojo zuwa Aso Rock don biyan sama da Naira miliyan 438 a matsayin kuɗin ƙwangila na wani kamfani da ke da alaka da shi da dakatacciyar ministar ta yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ministan ya ce kan ganawarsa da Tinubu?
Jaridar The Nation ta lura cewa ministan, lokacin da aka nemi hira da shi, kawai sai ya ce, "Komai daidai," yayin da yake fita daga fadar shugaban ƙasa.
An samu rahoton cewa Betta Edu ta biya kuɗin kwangila har N438.1m ga wani kamfani, New Planet Projects Limited wanda mallakin ministan harkokin cikin gida ne.
Sai dai a yayin da ake hira da shi a shirin "Siyasa A Yau" na Channels TV a daren ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, Tunji-Ojo ya wanke kansa daga zargin da ake masa.
Ministan ya ce duk da ya kafa kamfanin ne shekaru 10 da suka wuce, ya yi murabus daga shugabancinsa a shekarar 2019 lokacin da ya tsaya takarar majalisar wakilai.
Ministan harkokin cikin gidan ya bayyana rahoton a matsayin abin ban tsoro, inda ya bayyana cewa shi mai hannun jari ne kawai a kamfanin kuma baya shiga harkokinsa na yau da kullum.
Tunji-Ojo Ya Wanke Kansa
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya nesanta kansa daga badaƙalar kuɗin kwangilar N438m.
Ministan ya yi gaggawar musanya wannan ne ganin an dakatar da takwararsa, Dr. Betta Edu daga kujerar Ministar jin-kai ta kasa.
Asali: Legit.ng