Kano: Kotu Ta Mayar Ta Dayyabu Mijin Hafsat Gidan Yari Bisa Zargin Kashe Nafiu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Kano - Kotun Majistire da ke da zama a Yankaba, jihar Kano, ta sake garkame Dayyabu Abdullahi (mijin Hafsat), Adamu Muhammad da Nasidi Muhammad har zuwa ranar 18 ga watan Janairu.
Kotun ta sanya ranar 18 ga watan Janairu don ci gaba da sauraron shari'ar mutum uku da ake zargi da kashe wani Nafiu Hafizu, direban da ake zargin Hafsat (matar Dayyabu) ta kashe shi.
Ana tuhumar Hafsat da aikata manyan laifuka guda biyu, kisan kai da kuma yunkurin kashe kanta.
Amma dai ta musanya kashe mutumin duk da cewa ta amsa laifin kashe shi a rahoton da ta ba yyan sanda, a kokarin da ya yi na dakatar da ita daga yunkurin kashe kanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran mutum ukun suna fuskantar tuhuma kan laifuka uku da suka shafi hada baki don aikata ta'addanci, boye gaskiya da bayar da bayanan karya.
An gurfanar da Hafsat da mutum ukun a gaban babbar mai shari'a Hadiza AbdulRahman a ranar Laraba 27 ga watan Disamba, 2023, rahoton Daily Trust.
Mai shari'ar ta ba da umurnin ci gaba da tsare Hafsat a gidan gyaran hali har zuwa 1 ga watan Fabrairu.
Rabiu Sidi da Rabiu Abdullahi, lauyoyin wadanda ake karar sun roki kotu ta ba da belin mutanen, inda kotun ta ce zuwa 18 ga watan Janairu za ta duba yiyuwar hakan.
Asali: Legit.ng