Dangote Ya Farfado, Ya Ci Ribar da Ba a Yi Tsammani Ba a Cikin Kasa da Mako 1 Na 2024

Dangote Ya Farfado, Ya Ci Ribar da Ba a Yi Tsammani Ba a Cikin Kasa da Mako 1 Na 2024

  • Attajirin da ya fi kowa kudi a Najeriya kuma hamshakin attajirin nan na Afrika, Aliko Dangote, ya samu sama da dala miliyan 100 a cikin ‘yan kwanaki kadan a shekarar 2024
  • Hakan na zuwa ne bayan wani rahoto da ke cewa attajirin ya samu raguwar dala biliyan 3.6 a shekarar 2023 sakamakon faduwar darajar Naira
  • Tashin gaggawa na dukiyarsa ba zai rasa nasaba karfin hada-hadar da kamfanoninsa suka yi a kasuwar hannun jari ta NGX

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Najeriya - A makon farko na 2024, hamshakin attajirin nan na Najeriya, Aliko Dangote ya samu sama da dala miliyan 100, wanda ya daga darajar dukiyarsa ta haura dala biliyan 15, bayan faduwar dala biliyan 3.6 da ya yi a 2023.

Kara karanta wannan

Bayan cewa bai son a kai masa ziyara, Buhari ya yi kyautar galleliyar mota ga dan a mutunsa

Majiyar Legit ta ruwaito cewa, Aliko Dangote na nahiyar Afirka, shugaban masana'antun Dangote Plc, ya fara sabuwar shekara cikin nasara da hangen riba.

Dangote ya farfado daga rasa kudinsa na 2023
Dangote ya farfado daga asarar da ya yi | Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

An danganta wannan karuwa na dukiyar Dangote ne da rawar da hannun jarin kamfanoninsa suka yi a kasuwar hannayen jari ta Najeriya (NGX).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin samun kudin Dangote

Biliyan.Africa ta ba da rahoton cewa, wannan ya samo asali ne daga yadda kasuwa ta kaya a alkaluman hada-hadar hannun jari na cikin gida da ya kusanci maki 80,000.

Bloomberg Billionaires Index ta ruwaito cewa arzikin Dangote ya tashi daga dala biliyan 15.1 a farkon 2024 zuwa dala biliyan 15.2 ya zuwa lokacin da aka rubuta wannan rahoto.

Ribar dalar Amurka miliyan 106 da Dangote ya samu a bana ana alakanta ta da nasarorin na riba jarin hannayen NGX.

Hannayen jarin Dangote

Kara karanta wannan

Don burge Bankin Duniya: An tona asirin dalilin Tinubu na kara farashin mai da wutar lantarki

Hannun jarin da kamfanin Dangote ke da shi a kan muhimman masana’antun Najeriya ne ginshikan da suka tokare dawowar wani adadi daga arzikinsa.

Dangote ne ya mallaki 86% a babban kamfaninsa, Dangote Cement, 72.7% a kamfanin sukari na Dangote da kuma 66.5% a kamfanin NASCON Allied Plc mai sarrafa gishiri.

Hannun jarin da yake da shi a yanzu a NASCON Allied Plc da kuma kamfanin sukarin Dangote ya kai dala miliyan 108 da dala miliyan 624 bi da bi.

Matsayin Dangote a kudi a Afrika

An kiyasta kasonsa na mallakar kamfanin siminti mafi girma a Afirka, Dangote Cement, cewa ya kai dala biliyan 5.59.

Mujallar Forbes ta bayyana Dangote a matsayin mutum na biyu mafi arziki a nahiyar Afirka da ke da arzikin da ya kai dala biliyan 10.1.

Sai dai, Bloomberg ta bayyana shi a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Afirka da ke da arzikin da ya kai dala biliyan 15.2.

Kara karanta wannan

Bayin Allah sama da 100 sun mutu yayin da bama-bamai suka tashi a wurin taro kusa da Masallaci

Dangote zai fara tatar mai a Legas

A wani labarin, matatar Dangote mai karfin bpd 650,000 da ke Legas za ta samu zubin karshe na gangar danyen mai miliyan daya a ranar Litinin 8 ga watan Janairu, 2024, don fara aiki gadan-gadan a matatar.

Matatar ta karbi laya sau biyar na gangar danyen mai miliyan daya a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairun 2024 daga kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), kamar yadda majiyar Legit ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.