Bayan Cewa Bai Son a Kai Masa Ziyara, Buhari Ya Yi Kyautar Galleliyar Mota Ga Dan a Mutunsa

Bayan Cewa Bai Son a Kai Masa Ziyara, Buhari Ya Yi Kyautar Galleliyar Mota Ga Dan a Mutunsa

  • Tsohon shugaban kasa Buhari ya yi wata kyauta mai girma ga wani masoyinsa da ke zaune a garin Yashe na jihar Katsina
  • An ruwaito cewa, ya zuwa yanzu dai an ba shi mota, kudade da kuma buhunnan shinkafa har biyar don rage zafin kasar nan
  • A baya, Buhari ya ce ya yi farin ciki da cire tallafin mai domin yana tsammanin samun raguwar masu ziyara a gidan nasa da ke Daura

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Daura, jihar Katsina - Tsohon shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari ya gwangwaje wani dattijo da kyautar mota a ranar Asabar 6 ga watan Janairun 2024.

Wannan kuwa ya faru ne a lokacin da dattijon ya kai masa ziyara a gidansa da ke Daura, kamar yadda tsohon hadimin shugaban kasar ya bayyana.

Kara karanta wannan

'Ba zan lamunci rashin nasara daga gareku ba', Tinubu ya kyankyasa gargadi ga manyan sojojin kasa

A wani rubutu da Buhari Sallau ya yada a kafar Facebook ya ce, baya ga kyautar mota, dattijon ya tashi da buhunnan shinkafa biyar da kuma wani adadi na kudade.

Buhari ya yi kyautar mota
Ana tsaka da cece-kuce a kansa, Buhari ya yi kyautar mota | Hoto: Buhari Sallau, Mubarak Isa
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce, wannan dattijo mai kaunar tsohon shugaba Buhari ne, don haka aka ba shi damar ganin Manjo a gidan nasa da ke Daura.

Ta ina batun ziyarar ta fito?

A wallafar tasa, Sallau ya ce:

“A Jiya Asabar wadda tayi dai-dai da 6/01/2024. Wani tsoho ya samu damar ziyartar tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari, a gidansa dake Daura.
“Ziyarar ta samo asali ne domin kai masa wani cikakken masoyinsa na garin yashe wanda aka i sani da suna, (SAI BABA BUHARI) ko kuma (HARUNANMU), hakika tsohon shugaban kasa yaji dadi da kuma nuna farin cikinsa akan wannan masoyin nasa domin yaji duk irin soyayyar da yake masa da kuma hidima da yake akansa.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Bidiyon yadda limami ya rasu yana tsaka da jan sallah a masallaci ya dauki hankali

“Mai girma tsohon shugaban kasa ya gwangwaje dattijon da sabuwar mota kirar Golf 3, da kuma buhun shinkafa 5, da kuma wasu kudade.”

Na ji dadin cire tallafin man fetur, inji Buhari

sohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana jin dadinsa bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi.

Buhari ya ce kara kudin mai din ya rage yawan masu kai masa ziyara tun bayan barinsa kujerar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a jiya Lahadi 31 ga watan Disamba a birnin Katsina yayin wani taro da aka gudanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.