Tsohon Minista Ya Bayyana Dalilin da Ya Sa Ba Za a Kira Gwamnatin Buhari Matsayin Wacce Ta Gaza Ba
- Tsohon ministan ƙwadago da samar da ayyuka Chris Ngige, ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta gaza ba
- Ngige ya ce yana cikin gwamnatin Buhari kuma ya san yadda gwamnatin ta gudanar da ayyukanta
- Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce gwamnatin Buhari ta kammala aikin gadar Neja ta biyu, shirin ciyar da ɗaliban makarantu da kuma hanyoyin jiragen kasa da dama a faɗin ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Anambra - Tsohon ministan ƙwadago da samar da ayyuka, Chris Ngige, ya bayyana dalilin da ya sa ba za a iya bayyana mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin gazawa ba.
A cewar rahoton jaridar The Nation, Ngige ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta kammala ayyuka da dama a ƙasar nan.
Ya ambaci gadar Neja ta biyu, shirye-shiryen ciyar da ɗaliban makaranta, da filin jirgin sama na Enugu a matsayin wasu ayyukan da gwamnatin da ta shuɗe ta kammala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Chris Ngige ya kare gwamnatin tsohon Shugaba Buhari
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Alor a ƙaramar hukumar Idemili ta Kudu a lokacin rabon kayan tallafi ga ƴan jam’iyyar APC da naƙasassu da kuma tsofaffi, a ranar Asabar, 6 ga watan Janairu, jaridar The Punch ta ruwaito.
A kalamansa:
"Ba gaskiya bane cewa gwamnatin Buhari ta gaza. Ina cikin gwamnati kuma gwamnati ta kammala ayyuka da dama da suka haɗa da gadar Neja ta biyu, shirin ciyar da ɗalibai na makarantu da kuma hanyoyin jiragen ƙasa da dama a faɗin ƙasar nan."
Ngige Ya Faɗi Shirin APC Na Ƙwace Mulkin Anambra
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige, ya bayyana shirin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na karɓe ragamar mulkin wasu jihohin ƙasar nan
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana cewa jam'iyyar APC za ta ƙwace mulkin jihar Anambra a hannun jam'iyyar APGA a zaɓen shekarar 2025 mai zuwa.
Asali: Legit.ng