Yadda Likitan Jabu Ya Damfari Mai Sana'ar POS N21m

Yadda Likitan Jabu Ya Damfari Mai Sana'ar POS N21m

  • Rundunar ƴan sandan Najeriya ta kama Igwe Gift Okechukwu, wani likitan jijiyoyi na jabu bisa laifin aikata manya laifuka
  • An kama Okechukwu ne da laifin damfarar Anita Chinwe Mathias, wata mai POS a Owerri, jihar Imo, kan kuɗi naira miliyan 21
  • Rundunar ƴan sandan na tuhumar Okechukwu da laifuka da dama da suka haɗa da haɗa baki, safaran sassan jiki, aikata laifuka ta yanar gizo, damfara da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Rundunar ƴan sanda ta kama wani likitan jabu, Igwe Gift Okechukwu, bisa laifin damfarar Anita Chinwe Mathias, mai POS a Owerri, jihar Imo, naira miliyan 21.

Kakakin rundunar ƴan sandan Olumuyiwa Adejobi, a yayin da yake gabatar da wanda ake zargin a Abuja, ya bayyana cewa ana binciken Okechukwu bisa laifuka da dama da suka haɗa da, safarar sassan jiki, laifukan yanar gizo, sata, damfara, yaudara, zamba, da kuma satar bayanan sirri.

Kara karanta wannan

Dakarun ƴan sanda sun kama mutane 2,931 bisa zargin aikata laifuka fiye da 3 a jihar Kano

Yan sanda sun cafke likitan bogi
Yan sanda sun cafke likitan bogi kan damfarar mai POS Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Kamen Okechukwu ya biyo bayan rahoton da Mathias ta shigar gaban sashen binciken manyan laifuka na rundunar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana yadda Okechukwu, wanda ya bayyana kansa a matsayin Dr. Henry Ovie, likitan jijiyoyi a babban asibitin tarayya na Owerri, ya yaudare ta bayan ya shigar da wasu lambobi a na’urarta ta POS.

Okechukwu ya yi iƙirarin cewa yana jiran kuɗi kuma ya buƙaci ya yi amfani da POS na Mathias wajen yin ciniki.

Likitan na jabu ya tura Naira miliyan 5.5 zuwa asusunta domin gamsar da Mathias sahihancin sa.

Sai dai daga baya an bayyana cewa, wannan kuɗin da ya tura wani yunƙuri ne na yaudara, a cikin shirin damfarar da ya kitsa.

An bankaɗo laifukan Okechukwu

Adejobi ya bayyana cewa wanda ake zargin wanda ke bayyana kansa a matsayin likitan jijiya ya yi iƙirarin cewa kwanan nan ya samu sauyin wurin aiki daga Port Harcourt zuwa FMC, Owerri, ya fara gabatar da kansa ga mai POS ɗin ne a lokacin da suka haɗu da shi a wani kantin sayar da kayayyaki da ke Owerri.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun sanar sun kama masu shafin tsegumi na 'Gistlover', an saki hotuna

Okechukwu ya canza lambar wayarsa kuma ya tashi daga Owerri zuwa Lafiya a jihar Nasarawa, inda ya saya sabon wurin zama mai kyau.

Sai dai jami'an tsaro sun gano shi tare da kama shi a sabon wurin da ya ke.

Ya daɗe yana aikata miyagun laifuka

Rundunar ƴan sandan a cikin wata sanarwa ta ce:

"Bincike da aka yi ya nuna cewa wanda ake zargin yana da sunaye daban-daban kamar Igwe Richard, Ovie Henry da lambobin waya da imel da yake amfani da su wajen aikata munanan ayyukansa.”

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa, a binciken da aka gudanar, an gano cewa, ba a yi rajistar sunan Okechukwu a hukumar NIMC ba, kuma bayanansa ba sa cikin kowace ma’adanar bayanai ta Najeriya.

An gano cewa Okechukwu na da hannu wajen safarar sassan jiki. Bayan kama shi, an bayyana cewa yana da alaƙa da masu laifuka a birnin Toronto na ƙasar Canada, inda suka shiga sana’ar sayar da gabobin jikin bil’adama.

Kara karanta wannan

Asiri ya fara tonuwa: An kama mutum 8 da ake zargi da hannu a kisan bayin Allah sama da 150

Ƴan Sanda Sun Cafke Masu Laifuka a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta kama mutane 2,931 da ake zargi da laifin fashi da makami, garkuwa da mutane, kisan kai da sauran laifuka a sassan jihar a 2023.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Hussaini Gumel ya ƙara da cewa dukkanin waɗanda suka kama a shekarar da ta gabata sun gurfanar da su a gaban ƙuliya domin su girbi abinda suka shuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng