NNPC da Yan Kasuwa Sun Bayyana Matakin Karshe Kan Ƙara Farashin Litar Man Fetur a Najeriya

NNPC da Yan Kasuwa Sun Bayyana Matakin Karshe Kan Ƙara Farashin Litar Man Fetur a Najeriya

  • A karshe kamfanin mai na kasa NNPC da ƴan kasuwar mai sun kawo karshen raɗe-raɗin kara farashin litar man fetur a Najeriya
  • Ƴan kasuwa sun nuna cikakken goyon bayansu ga matakin NNPC na barin litar mai a kan N600 da N630 ba tare an samu ƙari ba
  • Bugu da ƙari, an warware batun cewa tallafin man fetur da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tsige, ya sake dawowa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya IPMAN, ta jaddada matsayar kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) cewa babu wani shiri na kara farashin litar fetur.

Shugaban IPMAN na ƙasa, Abubakar Maigandi, ne ya tabbatar da haka yayin da yake jaddada cewa farashin N600 da N630 kan kowace lita na nan daram babu ƙari.

Kara karanta wannan

"Babu lokacin murna" Shugaba Tinubu ya aike da zazzafan gargaɗi ga hafsoshin tsaron Najeriya

Farashin litar man fetur a Najeriya.
Daga Karshe, NNPCL da Yan Kasuwa Sun Cimma Matsala Kan Sabon Farashin Man Fetur
Asali: Facebook

A cewarsa, ba zasu sauya farashin litar man fetur ba matuƙar ba umarni suka samu daga kamfanin mai na ƙasa NNPC ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton The Nation ya tattaro Maigandi na cewa NNPCL na siyarwa ƴan kasuwa man fetur a farashin N568 kan kowace ƙiya ɗaya.

A kalamansa ya ce:

"Eh, riba kadan muke samu a kan abin da muke sayarwa a yanzu, amma sadaukarwa ce da ya kamata kowa ya yi don amfanin kasa.
“Ba mu samu wannan umarni na kara farashin daga kamfanin NNPCPL wanda shi ne kadai mai shigo da kaya ba."

Babu wani shiri na fara tsadar litar mai a Najeriya

Shima da yake magana, Billy Gillis-Harry, shugaban kungiyar masu sayar da man fetur ta kasa (PROOAN), ya tabbatar da matakin karshe kan farashin man fetur.

Da yake jawabi ga Arise TV, ya ce:

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya samu gagarumin goyon baya yayin da Kotun Koli ke dab da yanke hukunci

"Idan gwamnati ta e ta daina biyan tallafin fetur kuma har ta bari farashin lita ya tashi daga N480 zuwa N630, hakan na nufin iyakarsa nan ba zai wuce ba."
"Kuma kamfanin NNPCL na iya bakin ƙoƙarinsa wajen tabbatar da hakan, ya kamata mu yaba musu, mu jinjinawa kokarin da suke yi."

NNPCL ya tabbatar da babu shirin ƙara farashin fetur

Idan baku manta ba mun kawo muku rahoton cewa Gwamnatin tarayya ta hannun kamfanin mai na ƙasa NNPCL ta musanta raɗe-raɗin ana shirin ƙara farashin litar man fetur

A wata sanarwa da kamfanin mai NNPCL ya fitar ranar Laraba, ya buƙaci ƴan Najeriya su kwantar da hankulansu domin labarin ƙarin ba gaskiya bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262