Gwamnatin Tinubu Ta Amince da Kamfanonin Jiragen Sama 3 da Zasu Yi Jigilar Maniyyata Hajjin 2024
- Gwamnatin tarayya ta ware kamfanonin sufurin jiragen sama 3 da zasu yi aikin jigilar maniyya a aikin hajjin bana 2024
- Hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa (NAHCON) ce ta sanar da sunayen tare da kamfanonin jiragen da zasu yi jigilar kayan alhazai
- NAHCON ta raba wa kowane kamfani johohin da zai yi aiki, inda ta bai wa kamfanin Max Air kaso mafi tsoka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnatin Najeriya karkashin shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ta amince da kamfanonin jiragen sama guda uku da za su yi jigilar maniyyata aikin Hajji na 2024.
Kamfanonin jiragen da aka amince da su sune Air Peace Ltd., Max Air da kuma kamfanin sufurin jiragen sama na FlyNas na Saudiyya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Haka nan kuma gwamnatin Tinubu ta amince da kamfanonin dakon kaya waɗanda zasu yi jigilar kwaso kayayyakin alhazan Najeriya a aikin hajjin bana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanonin jiragen dakon kayan da aka amince da su sune, Cargo Zeal Technologies Ltd, Nahco Aviance da kuma Qualla Investment Limited.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Fatima Sanda Usara, mataimakiyar daraktan yaɗa labarai na hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa (NAHCON).
Yadda aka rabawa kamfanonin sufurin aiki a hajjin 2024
Sanarwan ta ce kamfanin Air Peace zai yi jigilar maniyyata daga jihohin Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Kuros Riba, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Imo, Kwara, Ondo da Ribas, da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Kamfanin jirgin saman Saudiyya FlyNas zai yi jigilar maniyyata daga jihohin Borno, Legas, Osun, Ogun, Neja, Sakkwato, Kebbi, Yobe da Zamfara, Daily Trust ta ruwaito.
Yayin da Max Air da ke da kaso mafi tsoka zai yi jigilar alhazai daga jihohin Bauchi, Benuwe, Kano, Katsina, Kogi, Nasarawa, Adamawa, Oyo, Taraba, Kaduna, Gombe, Jigawa da Filato.
Tinubu Ya Faɗi Babban Haɗari 1 Tal da Ke Tunkaro Najeriya
A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya hango babban haɗari na tunkaro Najeriya idan har ba a magance matsalar ƴan bindiga ba.
Shugaban kasar ya ce burin haɗa tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya ka iya shiga babban haɗari idan jami'an tsaro ba su yi da gaske ba.
Asali: Legit.ng