Hare-Haren Yan Bindiga: Shugaba Tinubu Ya Faɗi Babban Haɗari 1 Tal Da Ke Tunkaro Najeriya
- Bola Ahmed Tinubu ya hango babban haɗari na tunkaro Najeriya idan har ba a magance matsalar ƴan bindiga ba
- Shugaban kasar ya ce burin haɗa tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya ka iya shiga babban haɗari idan jami'an tsaro ba su yi da gaske ba
- Tinubu ya yi wannan furuci ne a taron bada bayanai kan yanayin tsaron ƙasa da ya gudana a Aso Villa ranar Jumu'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci hukumomin tsaron Najeriya su ƙara matsa kaimi kuma su gaggauta kakkaɓe ƴan bindigan da suka addabi jama'a.
Bola Tinubu ya yi gargaɗin cewa burin Najeriya na haɗa tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya zai shiga babban haɗari idan har matsalar ƴan bindiga ta ƙi ƙarewa.
Ya yi wannan jawabi ne ga hafsoshin tsaro da shugabannin hukumomin tattara bayanan sirri a taron ba da bayanai kan harkokin tsaro a Villa, Abuja ranar Jumu'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin hulɗa da jama'a, Fredrick Nwabufo, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a manhajar X.
Wannan jawabi na shugaba Tinubu na zuwa ne kwana ɗaya bayan ƴan bindiga sun kashe akalla mutum 17 tare da sace wasu 58 a kauyukan ƙaramar hukumar Kauru a Kaduna.
Haka nan kuma mayaƙan Boko Haram sun kashe Malamin coci a Kwari, karamar hukumar Geidam ta jihar Yobe.
Babban haɗarin da ke tunkaro Najeriya - Tinubu
Da yake jawabi ga hafsoshin tsaro ranar Jumu'a, 5 ga watan Janairu, 2024, Shugaba Tinubu ya ce:
"Muna kokarin cimma tattalin arzikin dala tiriliyan 1 a cikin ’yan shekaru masu zuwa, kuma kokarinmu zai samu naƙasu da shiga haɗari idan har ba mu gama kawo karshen hare-haren makiya ci gaba ba."
"Kullum yan Najeriya ƙara yarda da aminta suke yi da mu kuma suna jinjinawa sadaukarwan mazajen mu da mata. Nasarorin da kuka samu a fili suke kuma ƴan Najeriya sun shaida."
Tinubu Ya Aike da Zazzafan Gargadi Ga Hafsoshin Tsaro
A wani rahoton kuma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya faɗa wa hafsoshin tsaron ƙasar nan cewa ba ya wasa da rahotannin sirri ko kaɗan.
Tinubu ya ja kunnen hafsoshin tsaro da shugabannin hukumomin tattara bayanan sirri cewa gwamnatinsa ba zata lamurci gazawa ba.
Asali: Legit.ng