DHQ: Dakarun Sojojin Najeriya Sun Halaka Yan Bindiga Sama da 40, Sun Samu Gagarumar Nasara

DHQ: Dakarun Sojojin Najeriya Sun Halaka Yan Bindiga Sama da 40, Sun Samu Gagarumar Nasara

  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar sheƙe yan ta'adda 43 tare da kamo wasu sama da 100 a samame daban-daban cikin mako ɗaya
  • Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ce yanzu sojoji suna bin yan bindiga har cikin dajin da suke ɓuya, su halaka su
  • Kakakin DHQ, Manjo Janar Buba, ya bayyana irin nasarorin da sojoji suka samu da kwazon da suka yi a makon jiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hedikwatar tsaro (DHQ) ta ce akalla ‘yan ta’adda 43 ne sojoji suka kashe, kana suka kama wasu 115 a samame daban-daban da suka kai a cikin mako guda da ya gabata.

Daraktan yada labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Mutum uku da aka sace sun mutu a kokarin gudowa daga hannun yan bindiga

Sojoji sun murƙushe yan ta'adda 43 a mako ɗaya.
DHQ: Dakarun Sojojin Najeriya Sun Halaka Yan Ta'adda 43, Sun Kamo 115 Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Mista Buba ya ce sojoji sun mayar da hankali a yakin da suke yi da masu tada kayar baya da kuma kokarin kakkabe sauran masu aikata laifuka a fadin kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, dakarun sojojin Najeriya a yanzu suna farautar 'yan ta'adda har cikin daji inda maboyarsu take tare da kai masu zafafan hare-hare da nufin halaka su.

An kashe manyan hatsabiban yan ta'adda

Ya ce sojojin sun yi nasarar halaka wasu manyan shugabannin 'yan ta'adda da mayaƙansu masu ɗumbin yawa, tare da rage musu karfin da suke taƙama da shi.

A ruwayar PM News, Buba ya ce:

"A cikin mako ɗaya da muke magana a kai, dakarun sojoji sun kai harin kwantan bauna, samame, yakin sunƙuru da sauran nau'ikan hare-hare kan 'yan ta'adda ba kakkautawa.
"Wadannan ayyukan luguden wuta sun samar da sakamako mai kyau, inda suka zama sanadin kashe 'yan ta'adda 43 tare da kama wasu 115.

Kara karanta wannan

Sojojin Sama Sun Kashe Shugaban Yan Ta'adda, Ba'a Shuwa, da Wasu Mayakansa a Borno

"Sojojin sun kwato makamai iri-iri 87 da alburusai 666 da suka hada da bindigogi kirar AK-47 guda 11, bindiga kirar FN daya, bindigogin Pump guda biyu da kuma bindigogin gida guda takwas."

Buba ya kara da cewa, sojojin sun kuma kama barayin ɗanyen mai 17 tare da ceto mutane 39 da aka yi garkuwa da su a yankin Kudu maso Kudu.

Gawar marigayi gwamnan Ondo ta iso Najeriya

A wani rahoton kuma Gawar marigayi gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ta iso gida Najeriya yau Jumu'a, 5 ga watan Janairu, 2024.

An dawo da gawar marigayi tsohon gwamnan ne daga ƙasar Jamus, inda ya rasu bayan fama da doguwar jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262