Allahu Akbar: Mutum uku da aka sace sun mutu a kokarin gudowa daga hannun yan bindiga
- Wasu mutum uku da suka faɗa hannun masu garkuwa da mutane sun mutu a kokarin gudowa daga sansanin yan bindiga
- Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma a majalisar dattawa, Sunday Karimi, ne ya bayyana haka a Lokoja ranar Jumu'a
- Ya yi kira ga rundunar yan sanda da hukumar tsaron farin kaya DSS sun tashi tsaye wajen kare rayukan al'umma
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Sanata Sunday Karimi, ya ce mutane uku a mazaɓarsa sun rasu yayin da suke kokarin tserewa daga hannun ƴan bindiga.
Sanatan ya bayyana haka ne a Lokoja, babban birnin jihar Kogi ranar Jumu'a, 5 ga watan Janairu, 2023, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce lamarin ya faru ne a tsakanin kauyukan Idofin da Isanlu a karamar hukumar Yagba ta Gabas da ke cikin jihar Kogi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karimi ya bayyana damuwarsa kan yadda ake ci gaba da samun kes ɗin garkuwa da mutane a mazabar da yake wakilta, ba tare da jami’an tsaro sun ɗauki mataki ba.
Ya kuma jaddada cewa an yi garkuwa da sama da mutane shida a cikin sa'o'i 48 da suka gabata a yankunan da wannan lamarin ya shafa.
A rahoton Daily Post, Sanatan ya ce:
"Mutane uku kuma sun rasa rayukansu a Idofin da Isanlu a kokarin tserewa daga sansanin masu garkuwa da mutane."
Karimi ya aike da sako ga jami'an tsaro
Bisa haka ne Sanatan ya yi kira ga kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi, CP Bertrand Onuoha, da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da su kara kaimi wajen tabbatar da tsaro a yankunan.
Rahotannin da suka fito daga yankin da Sanata Karimi ke magana a kai ya nuna cewa a halin yanzu mazauna na rayuwa ne cikin tsoro da fargabar abin da ka iya zuwa ya dawo.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO), SP William Aya, ya yi alkawarin nemo cikakken bayani kan lamarin kamar yadda Sanatan ya yi ikirari.
Yan Bindiga Sun Halaka Yan Kasuwa Shida a Jihar Katsina
A wani rahoton kuma Yan bindiga sun kashe ƴan kasuwa shida yayin da suke hanyar zuwa cin kasuwar mako-mako a jihar Katsina.
Yan ƙasuwar sun baro kauyen Maidabino da nufin zuwa kasuwar Yantumaki, kwatsam suka yi gamo da yan bindiga.
Asali: Legit.ng