Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Ayarin 'Yan Kasuwa Wuta, Sun Kashe Mutane da Yawa a Jihar Katsina
- Yan bindiga sun kashe ƴan kasuwa shida yayin da suke hanyar zuwa cin kasuwar mako-mako a jihar Katsina
- Yan ƙasuwar sun baro kauyen Maidabino da nufin zuwa kasuwar Yantumaki, kwatsam suka yi gamo da yan bindiga
- Ganau sun bayyana cewa kafin jami'an tsaro su kariso har yan bindigan sun kashe wasu, babu tabbacin ko sun sace wasu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Akalla ’yan kasuwa shida ne suka rasa rayukansu a ranar Juma’a yayin da ayarin motocinsu suka gamu da ‘yan bindiga a karamar hukumar Danmusa ta Jihar Katsina.
’Yan kasuwar sun taso ne daga kauyen Maidabino da nufin zuwa cin kasuwar mako-mako da ke garin Yantumaki.
Dukkan ƙauyukan guda biyu suna karkashin ƙaramar hukumar Ɗanmusa ne a jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma, kamar yadda Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna yankin sun bayyana cewa a ko wane lokaci ’yan kasuwar sun saba tafiya a cikin ayari saboda matsalar tsaron da ake fama da ita a ƙaramar hukumar.
Yadda lamarin ya faru
An tattaro cewa, ayarin motocin da ke dauke da ‘yan kasuwar sun ci karo da yan bindigan ne suna daf da shiga Yantumaki.
Mazauna yankin sun kara da cewa kwatsam ba zato ba tsammani yan bindigan suka fito daga wani daji, suka fara harbin motocin, Premium Times ta ruwaito.
Daya daga cikin mazauna yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:
"Da sanyin safiya lokacin da ‘yan kasuwan suka zo kusa da Yantumaki kwatsam ‘yan bindigan suka fito daga wani daji suka mamaye babbar hanya.
"Maharan sun buɗe wa ayarin motocin wuta kuma a lokacin da jami'an tsaro da suka haɗa da sojoji da ƴan sanda suka ƙariso wurin an riga an kashe yan kasuwa 6.
"Har yanzun dai bamu sani ba ko ƴan bindigan sun yi nasarar sace wasu daga cikin ƴan kasuwar ko akasin haka."
Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, ASP Abubakar Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani ba.
Yan sanda sun kama mutum 8 a jihar Filato
A wani rahoton Dakarun yan sanda sun kama mutum 8 da ake zargin suna da alaƙa da kashe-kashen da aka yi a kananan hukumomin jihar Filato.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda na jihar, DSP Alfred Alabo, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa ranar Jumu'a.
Asali: Legit.ng