Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutum 7 Yan Gida Daya, Sun Tafka Barna a Abuja
- Yan bindiga sun kara zafafa kai hare-hare kauyukan da ke kewaye da ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayya
- Yan sanda biyu sun ji raunuka yayin da wasu yan bindiga suka yi garkuwa da mutum bakwai yan gida ɗaya a Abuja
- Wani mazaunin Bwari ya ce maharan sun yi musayar wuta da dakarun yan sanda kuma sun kashe wani mai suna Alhaji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Wasu tssgerun ƴan bindiga sun yi awon gaba da mutum 7 ƴan gida ɗaya yayin da suka kara zafafa kai hare-hare yankin Bwari a birnin tarayya Abuja.
Haka nan kuma wasu dakarun ƴan sanda guda biyu sun ji raunukan harbin bindiga a kokarin dakile yunkurin ƴan bindigan.
Daily Trust ta tattaro cewa ‘yan bindiga sun harbe wani mutum mai matsakaicin shekaru, mai suna Alhaji, har lahira wanda ya jagoranci ‘yan sanda wajen dakile garkuwa da mutanen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun nuna cewa a ƴan kwanakin nan, ƴan bindiga sun matsa kaimi wajen kai hare-hare kauyukan yankin ƙaramar hukumar Bwari, suna kisa da garkuwa da mutane.
Yadda yan bindigan suka raunata ƴan sanda biyu
Wani mazaunin Bwari, Isaiah Samuel, yayin hira ta wayar tarho, ya shaida wa wakilin jaridar cewa lamarin ya auku ne da safiyar ranar Laraba.
Ya ce lokacin da maharan suka kutsa kai Zuma 1 a tsakiyar Bwari, sai suka rarrabu zuwa wurare daban-daban bayan sun gano gidan mutanen da suke hari.
Bayan yan gida ɗayan sun fahimci bakin fuska a wuraren gidansu, sai suka kira wani ɗan uwansu mai suna Alhaji (wanda yan bindigan suka kashe).
"A lokacin da mutumin ya yi zargin wani bakon fuska a kofar gidansa, nan take ya kira dan uwansa, wanda aka fi sani da Alhaji domin ya sanar da ‘yan sanda,” inji shi.
An ce Alhaji ya taho tare da tawagar ‘yan sanda zuwa gidan ne yayin da daya daga cikin ‘yan bindigar da ke boye a wani lungu ya harbe shi har lahira.
Samuel ya ce, nan take ‘yan sandan suka fara musayar wuta da ‘yan ta’addan, lamarin da ya sa biyu daga cikin jami’an suka samu raunuka.
Samuel ya ƙara da cewa:
“A karshe maharan sun yi nasarar tafiya da mutumin da ‘yan uwansa, saboda nisan da ke tsakanin gidan da wurin da ƴan sanda suka tsaya suna fafatawa da su."
Luguden Wutan Jirgin NAF Ya Halaka Shugaban Ƴan Ta'adda
A wani rahoton na daban Luguden wutan jirgin sojojin Najeriya ya halaka shugaban ISWAP, Ba'a Shuwa da wasu mayaƙansa a jihar Borno.
Zagazola Makama ya ce sojoji sun sami wannan nasara ne yayin wani samame da suka kai ranar 2 ga watan Janairu, 2024.
Asali: Legit.ng