Nasara: Hatsabiban 'Yan Bindiga Sun Sheƙa Lahira Yayin da Sojoji Suka Far Musu a Jihohin Arewa Biyu
- Dakarun sojoji sun samu nasarar halaka hatsabiban yan bindiga tare da ceto mutame daga hannunsu a Zamfara da Katsina
- Kakakin rundunar Operation Hadarin Daji, Kaftin Ibrahim Yahaya, ya ce sojojin sun halaka yan bindiga 10, sun kwato muggan makamai
- A cewarsa, waɗanda aka ceto sun haɗa da mata da jarirai kuma tuni aka sake haɗa su da ƴan uwansu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
'Yan bindiga 10 sun baƙunci lahira yayin da aka kubutar da mutane tara a wani samame da sojoji suka kai a jihohin Katsina da Zamfara da ke Arewa maso Yamma.
Dakarun sojojin hadin gwiwa na rundunar Operation Hadarin Daji (OPHD) da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Arewa maso Yamma ne suka samu wannan nasara ranar Laraba.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Operation OPHD, Kaftin Ibrahim Yahaya, ya fitar kuma rundunar soji ta ƙasa ta wallafa a manhajar X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kyaftin Yahaya ya ce an kwato makamai da alburusai da suka hada da babur din da suke aiki da na’urorin sadarwa daga hannun ‘yan ta’addan.
Ya ce:
“Ranar 3 ga watan Janairun 2024, rundunar sojin ta kai wani samame kan ‘yan ta’adda a maɓoyarsu a karamar hukumar Batsari da Safana ta jihar Katsina.
"Yayin wannan samamen sojojin sun kashe 10 daga cikin ‘yan ta’addan, yayin da sauran suka gudu da raunukan harbin bindiga.
"Sojojin sun kwato bindiga AK-47 guda daya, alburusai, bindigogin Danish 7, bindigogi na gida guda 3, da sauran muggan makamai da na’urorin sadarwa, wayoyin hannu, da kakin soja yayin da aka kwato babura 4.”
Yadda sojojin suka ceto mutane 9
Kakakin OPHD ya ƙara da cewa dakarun sun ceto mutane 9 a wani samame da suka kai a kauyukan Dansadau da Dandalla da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Yahaya ya ci gaba da cewa:
"Yan bindigan sun gudu sun bar mutanen bayan musayar wuta da sojoji. Kuma tuni aka maida waɗanda aka ceto cikin iyalansu."
Mutanen da sojojin suka kubutar sun haɗa da mata biyar da jarirai guda huɗu.
Miyagu Sun Halaka Babban Limamin Jumu'a
A wani rahoton kun ji cewa Wasu tsageru sun halaka babban limamin Masallacin Jumu'a da wani ɗan acaba a sabon harin da aka kai jihar Filato.
Shugaban ƙungiyar Fulani GAFDAN, Garba Abdullahi, ya ce tuni aka sanar da jami'an tsaro abin da ya faru don ɗaukar mataki.
Asali: Legit.ng