Kano: Abba Kabir Ya Dauki Muhimmin Mataki Bayan Ya Amince Da Biyan Diyyar Rusau

Kano: Abba Kabir Ya Dauki Muhimmin Mataki Bayan Ya Amince Da Biyan Diyyar Rusau

  • Yayin da ke ci gaba da shari'a kan rusau a Kano, Gwamna Abba Kabir ya fara biyan kudaden ga wadanda abin ya shafa
  • Abba ya fara biyan naira biliyan daya daga cikin biliyan uku da ya amince zai biya diyyar tun farko a jihar bayan an maka shi a kotu
  • Tun farko, Kotun ta umarci gwamnan ta biya naira biliyan 30 kudin diyya bayan gwamnan ya rushe musu shaguna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya fara biyan kudaden diyyar rusau a jihar.

Gwamnan ya fara biyan naira biliyan daya ne daga cikin uku da ya amince zai biya, kamar yadda Tribune ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ku sake ba ni dama: Tsohon gwamnan Arewa ya fadi darussan da ya koya a gidan kaso, ya tura bukata

Gwamna Abba Kabir ya fara biyan diyyar rusau biliyan daya
Abba Kabir ya fara biyan kudaden diyyar rusau a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Twitter

Wane hukunci kotun ta yanke a baya?

Wannan na zuwa ne bayan masu shaguna da kungiyar 'yan kasuwa sun maka gwamnan a kotu kan rusau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun yayin hukuncinta, ta umarci gwamnan ta biya naira biliyan 30 kudin diyya bayan gwamnan ya rushe musu shaguna.

Gwamna Abba ya yi rushe-rushe da dama tun bayan hawanshi karagar mulki da ya ke ganin an mallaka ko gina su ba bisa ka'ida ba.

Mene kungiyar ke cewa kan rusau din a Kano?

Kungiyar masu shaguna masallacin Idi (MEOTA) ta bayyana cewa mutane fiye da 30 sun mutu yayin rusau din da kuma bayanta, cewar TheCable.

Da yake magana a madadin kungiyar, Barista Maaruf Mohammed ya ce duk da fara biyan kudaden, kungiyar ta shigar da gwamnatin kara ga hukumar 'yan sanda.

Kungiyar ta kai karar ce kan zargin laufukan da aka aikata yayin rusau din da aka gudanar.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Mutum uku da aka sace sun mutu a kokarin gudowa daga hannun yan bindiga

Abba Kabir ya amince da biyan biliyan 3 na rusau

A wani labarin, Gwamna Abba Kabir ya amince da biyan diyyar naira biliyan 3 na rusau da aka gudanar a jihar.

Kungiyar 'yan kasuwa da masu shaguna a masallacin Idi sun maka gwamnan a kotu kan rusau da aka yi wanda ya jawo asara a jihar.

Kotun yayin hukuncinta, ta umarci gwamnan ya biya diyyar naira biliyan 30 ga wadanda abin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.