Rusau: Yan Kasuwan Kano Sun Shigar da Korafi Wurin Yan Sanda Kan Gwamna Abba da Kwankwaso

Rusau: Yan Kasuwan Kano Sun Shigar da Korafi Wurin Yan Sanda Kan Gwamna Abba da Kwankwaso

  • Ƙungiyar masu shaguna da ƴan kasuwar Masallacin Idi sun kai ƙarar Gwamna Abba da Rabiu Kwankwaso gaban kwamishinan ƴan sandan Kano
  • Ƙungiyar ta kai ƙarar ne bisa rushe musu wuraren neman abincinsu da gwamnatin jihar ta yi ba bisa ƙa'ida ba
  • A cikin ƙarar ta su sun buƙaci kwamishinan da ya gudanar da cikakken bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Ƙungiyar masu shaguna da ƴan kasuwar Masallacin Idi sun kai ƙara gaban kwamishinan ƴan sandan Kano, Mohammed Usaini Gumel, inda suka nemi a binciki yadda gwamnatin jihar ta lalata musu shaguna.

Jaridar Daily Trust ta ce ƙungiyar dai ta shigar da ƙarar ne a kan Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Rabiu Musa Kwankwaso, Abdullahi Baffa Bichi, Muhammad Diggol da sauransu.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin jami'o'in kasashen waje da gwamnatin Tinubu ta haramta a Najeriya

yan kasuwa sun kai karar Gwamna Abba
Rusau: Yan Kasuwan Kano Sun Shigar da Korafi Wurin Yan Sanda Kan Gwamna Abba da Kwankwaso Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Lauyan kungiyar, Maaruf Muhammad Yakasai, ya ce ƙarar da ƙungiyar ta shigar a hukumance ta samo asali ne a kan haɗa baki, sata, almubazzaranci da kuma ɓarna da ya saɓawa sashe na 97, 286, 308 da 326 na dokokin hukunta manyan laifuka na jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa suka shigar da ƙorafin?

Ƴan kasuwan sun shigar da ƙorafin ne kan yadda gwamnatin jihar ta rusa musu shagunansu ba tare da bin ƙa'ida ba.

Ƴan kasuwar sun bayyana cewa tun kafin zaɓen gwamnan jihar Kano, waɗanda ake zargin suka sha alwashin rushe shagunan na su.

Sun bayyana cewa bayan jam'iyyar NNPP ta yi nasara a zaɓen gwamnan Kano, Gwamna Abba ya kafa kwamiti wanda ya jagoranci rushe shagunansu ba tare da an sanar da su ba.

Ƴan ƙasuwar sun ƙara da cewa hakan ya jawo musu asarar ɗumbin dukiya wacce ta kai N250bn, sannan da yawa daga cikinsu suka kwanta rashin lafiya, ciki har da masu ciwon sashi, saboda kaɗuwa kan asarar da suka yi.

Kara karanta wannan

Ba a gama jimamin mutuwar mutum 190 ba, yan bindiga sun sake kai mummunan hari a jihar Plateau

Me nene buƙatar ƴan kasuwan?

Lauyan ya zayyano buƙatun ƴan kasuwar kamar haka:

"Muna roƙon ma’aikatunku na gari da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin, musamman ta fuskar laifukan da suka shafi dukiyoyi da kuma bil’adama, domin wasu sun rasu, wasu kuma ba su da lafiya sakamakon azabtarwa, masu hannu da shuni yanzu sun zama talakawa.
"Muna buƙatar a binciki laifin sannan waɗanda aka samu da aikata laifin su fuskanci fushin hukuma.
"A shirye mu ke a lokacin da ya dace na gudanar da bincike domin samar da dukkan hujjoji da bayanan da ke hannunmu don tabbatar da zargin da ake yi wa waɗanda ake tuhuma."

Gwamna Abba Ya Fara Biyan Kuɗin Diyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fara biyan kuɗaɗen diyyar rusau.

A cikin N3bn da gwamnan zai biya saboda rusau ɗin shagunan ƴan kasuwa da ya yi, ya fara bayar da N1bn

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng