Rundunar Yan Sandan Jihar Kano Ta Yi Caraf da Likitan Bogi Mai Zubar da Juna Biyu

Rundunar Yan Sandan Jihar Kano Ta Yi Caraf da Likitan Bogi Mai Zubar da Juna Biyu

  • Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi caraf da wani likitan bogi wanda ya ƙware wajen zubar da ciki a jihar
  • Likitan bogin mai suna Chidera Ugwu ya shiga hannu ne bayan ya yi yunƙurin zubar da cikin wata matashiya inda daga ƙarshe ya halaka ta
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano wanda ya tabbatar da cafke likitan bogin ya bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa tuhumar da ake masa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Jami’an ƴan sanda a jihar Kano sun cafke wani likitan bogi, mai suna Chidera Ugwu, da ake zargin ya yi sanadiyyar rasuwar wata matashiya.

Jaridar Daily Trust ta ce ana zargin Chidera Ugwu ne dai da yi wa matashiyar mai ɗauke da juna allurai da ɓata ƙwayoyi waɗanda suka yi sanadiyyar rasuwarta.

Kara karanta wannan

An cafke babban kwamandan sojoji bisa hannu kan hare-haren Plateau? Gaskiya ta bayyana

Yan sanda sun cafke likitan bogia Kano
Likitan bogi ya shiga hannun ƴan sanda a Kano Hoto: Kano State Police Command
Asali: Facebook

Sanar da cafke Chidera dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanya wa hannu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka cafke likitan bogin

Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa wani Nura Balarabe ya kai ƙarar wani matashi mai suna Ukasha Muhammed mai shekara 19 da haihuwa mazaunin ƙauyen Langel da ke ƙaramar hukumar Tofa a gaban ƴan sanda.

Nura ya kai ƙarar matashin ne bayan ya yi wa ƙanwarsa ciki mai suna Amina ƴar shekara 19 da haihuwa a duniya. Bayan ya yi wa matashiyar ciki ya kuma garzaya wajen likitan bogin domin neman taimako.

Sanarwar ta ce Ugwu, mai shekaru 24 wanda ke zaune a Lanbum Banki a ƙaramar hukumar Tofa ya yi allurar ne da nufin zubar da cikin amma hakan ya yi sanadiyyar mutuwar Amina.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin jami'o'in kasashen waje da gwamnatin Tinubu ta haramta a Najeriya

Kiyawa ya ce an kama waɗanda ake zargin kuma sun amsa laifin da ake tuhumar su da shi, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Binciken da ƴan sandan suka gudanar ya nuna cewa likitan na jabu ya dade yana yi wa mata masu juna biyu alluran da ke da mugun haɗari.

Ɗan Daba Ya Halaka Limami a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ɗan daba ya halaka wani limamin masallaci har lahira a unguwar Jakara dake cikin birnin Kano.

Ɗan daban mai suna Yusuf Haruna wanda aka fi sani da suna Lagwatsami ya halaka limamin ne bayan ya hana su shan wiwi a kusa da masallaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng