“Manyan Coci Za Su Ruguje”: Jerin Malamai 2 da Suka Hangowa Kiristoci Matsala a 2024

“Manyan Coci Za Su Ruguje”: Jerin Malamai 2 da Suka Hangowa Kiristoci Matsala a 2024

Fastocin Najeriya sun yi kaurin suna wajen hasashen abubuwa daga lokaci zuwa lokaci da hango abubuwan da za su faru a gaba. A ranar Litinin, 1 ga watan Janairu, wanda ya yi daidai da shekarar 2024, malaman Kirista a fadin kasar sun yi hasashensu game da sabuwar shekarar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Fastoci da dama a ranar Litinin sun yi magana game da makomar yan Najeriya a hannun yan siyasa. Hasashen siyasa da dama ya karkata ne a kan Shugaban kasa Bola Tinubu da sabuwar gwamnati.

Malaman addini a Najeriya
“Manyan Coci Za Su Ruguje”: Jerin Malamai 2 da Suka Hangowa Kiristoci Matsala a 2024 Hoto: Bishop Joseph Edoro, Prophet Joshua Iginla
Asali: Twitter

Sai dai kuma, kimanin fastoci biyu ne suka yi hasashe kan babban kalubalen da ke gaban mabiya addinin kiristanci a sabuwar shekarar.

Bishop Joseph Edoro

Kara karanta wannan

Digirin bogi: Ina cikin damuwa game da tsarona, in ji dan jaridar da ya saki rahoton 'digiri dan Kwatano'

Faston mazaunin Lagas kuma shugaban majami'ar 'A Touch From Heaven International Ministry', Bishop Joseph Edoro, ya yi hasashen cewa manyan coci za su fuskanci gagarumin matsala a 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata hira da jaridar Independent, malamin addinin ya magantu kan abun da Ubangiji ya nuna masa, yana mai cewa yan Najeriya su yi tsammanin ganin manyan coci sun rarrabu zuwa kanana.

Yayin da yake kokawa kan gazawar shugabanni a kasar a 2024, malamin addinin ya ce a 2024, "manyan coci za su ruguje da rarrabuwa".

Prophet Joshua Iginla

Da yake jawabi ga dubban mabiyansa a safiyar Litinin, Prophet Joshua Iginla na cocin Champions Royal Assembly da ke Abuja ya yi hasashen cewa cocina za su rabu tsakanin 2024 da 2026 kuma fastoci za su tsani junansu kamar yadda suka tsani iblis.

Kara karanta wannan

2023: Muhimman abubuwa 10 da suka faru a Majalisar Tarayya a shekarar da ta wuce

Malamin addinin ya yi hasashen koma baya a addinin Kiristancin, yana mai cewa "asirin manyan malamai da dama zai tonu". Ya jaddada cewa hakan zai girgiza imanin matasa a coci.

A cewarsa, coci zai fuskanci abubuwa da dama da ba za su fadu ba, sannan imanin mutane da dama zai samu rauni saboda haka.

Kalli bidiyon hasashen Iginla a kasa:

Malami ya gargadi Tinubu

A wani labarin kuma, mun ji cewa an gargaɗi Shugaba Bola Tinubu kan abubuwa uku da ka iya faruwa da shi da gwamnatinsa a 2024.

Fasto Joshua Iginla na cocin Champions Royal Assembly dake Abuja ya gargaɗi shugaban ƙasar a cikin hasashensa na 2024 yayin da ya yi hasashen cewa darajar Naira za ta cigaba da faɗuwa a sabuwar shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng