Babban Malamin Addini Ya Gargadi Tinubu Kan Abubuwa 3 a Sabuwar Shekara

Babban Malamin Addini Ya Gargadi Tinubu Kan Abubuwa 3 a Sabuwar Shekara

  • An gargaɗi shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya kula da lafiyarsa a shekarar 2024 domin kaucewa matsalar rashin lafiya ta gaggawa
  • Fasto Joshua Iginla ya yi gargaɗin cewa ya kamata shugaban ƙasa ya shirya cin amana a tsakanin amintattun aminansa kuma ya mutunta ra’ayin matarsa
  • A cikin hasashensa na sabuwar shekara, Iginla ya yi hasashen cewa Naira za ta ci gaba da taɓarɓarewar akan dalar Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - An gargaɗi Shugaba Bola Tinubu kan abubuwa uku da ka iya faruwa da shi da gwamnatinsa a 2024.

Fasto Joshua Iginla na cocin Champions Royal Assembly dake Abuja ya gargaɗi shugaban ƙasar a cikin hasashensa na 2024 yayin da ya yi hasashen cewa darajar Naira za ta cigaba da faɗuwa a sabuwar shekara.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya kori SSG Abdullahi Baffa Bichi? Gaskiya ta bayyana

Fasto Iginla ya gargadi Tinubu
Fasto Iginla ya aike da gargadi uku ga Shugaba Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Prophet Joshua Iginla
Asali: Twitter

Idan ba a manta ba Fasto Iginla ya yi hasashen nasarar Shugaba Tinubu a 2022, kafin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kuma zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dole ne Tinubu ya kula da lafiyarsa

A cikin sakonsa a safiyar Litinin, 1 ga watan Janairu, Fasto Iginla ya yi gargaɗin cewa dole ne shugaban ƙasar ya kula da lafiyarsa don kaucewa "taɓarɓarewar lafiyarsa sau biyu" a cikin sabuwar shekara.

Daga nan malamin addinin ya yi addu’ar Allah ya ɗora shugaban ƙasan a kan hanyar daidai.

Cin amanar gwamnatin Tinubu

Ya kuma gargaɗi Shugaba Tinubu kan amintattun abokansa. Fasto Iginla ya ce an bayyana masa cewa wasu amintattun shugaban ƙasar za su yi masa rashin aminci, kuma daga ƙarshe za su ci amanarsa.

Kara karanta wannan

Muhimmin abu 1 tak da ya sa ake ganin ya kamata shugaban hukumar zaɓe INEC na ƙasa ya yi murabus

Faston ya yi nuni da cewa akwai yiwuwar wasu daga cikin abokan Shugaba Tinubu za su zama maƙiyansa.

Ruhin fahimta na Oluremi Tinubu

A cikin jawabin nasa, Iginla ya gargaɗi Shugaba Tinubu da kada ya raina shawarar matarsa, Oluremi, yana mai cewa uwargidan shugaban kasan tana da ruhin fahimta a tattare da ita.

Iginla ya bayyana cewa:

"Akwai ruhin fahimta ga uwargidan shugaban ƙasa, kada shugaban ƙasa ya watsar da shawarwarinta."

Ku kalli bidiyon a nan ƙasa:

Iginla Ya Yi Abin da Zai Faru a 2024

A wani labarin kuma, kun ji cewa Fasto Joshua Iginla ya yi hasashen abubuwan da za su faru a shekarar 2024.

Babban faston ya yi hasashen cewa tsakanin 2024 da 2026, mutane a faɗun duniya za su fuskanci gagarumin sauyi a yanayin zafi da yanayi gaba ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng