Budurwa Ta Koka Yayin da Saurayi Ya Yasar da Ita a Filin Jirgin Sama, Tana Neman Taimako
- Bidiyon wata matshiyar budurwa da ta makale a filin jirgin sama ya yadu a soshiyal midiya kuma ya haddasa cece-kuce
- Matashiyar ta bada sunan filin jirgin saman da aka yasar da ita a cikinsa, tana mai kokawa cewa bai zo daukarta ba kamar yadda ta yi tsammani
- Yayin da wasu suka tausaya mata kan halin da ta tsinci kansa, wasu sun caccaki budurwa kan rashin kasancewa da kudi a hannu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wata matashiya ta koka a soshiyal midiya bayan da saurayinta ya yi watsi da ita a filin jirgin sama.
A cikin wani bidiyo da ya samu mutum fiye da miliyan hudu a TikTok, @datgirl_dime ta ce ya ki zuwa ya dauke ta.
Da aka tambayeta game da inda take, @datgirl_dime ta bayyana cewa a Fort Lauderdale, wani birni a Flirida, kasar Amurka ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bidiyonta mai karya zuciya na zuwa jim kadan bayan wani bidiyo da ta yana inda take murnar cewa sahibinta ne ya biya mata kudin jirgi don ta je ta gan shi.
A bidiyon, ta ce ya aikata hakan ne saboda ya yi kewanta.
Kalli bidiyon a kasa:
Mutane sun taysaya mata
Lex-Justice ta ce:
"Shin kina da kudin, kin biya kudin jirginki da dakinki da kanki? Ki dunga yawo da kudinki a kodayaushe don idan irin haka ya faru ki ji dadinki."
piscesvxn ta ce:
"Irin wannan ya faru da ni a NYC sai da na kama dakin otal dina na tsawon kwanaki biyu."
Esperanza ya ce:
"Kina lafiya yarinya zan iya lulawa da ke waje mu ji dadinmu ina zaune ne a Wisconsin."
kiyaaa ta ce:
"Ina fatan kina lafiya yarinya! kina da matukar kyau."
Ango ya fasa aure ana gab da biki
A wani labarin, mun ji cewa wasu iyali a kauyen Sokyot, gudunmar Kipkaren da ke mazanar Mosop, Nandi sun samu karayar zuciya bayan angon diyarsu ya fasa aurensu ana gab da biki.
Da take zantawa da kafar labarai ta kasar Kenya, TUKO.co.ke, wata yar kauyen su amaryar ta bayyana cewa masoyan sun shirya gudanar da shagalin kafin bikinsu a ranar 22 ga watan Disamba, amma hakan bai samu ba.
Asali: Legit.ng