NNPCL Ya Yi Maganar Maida Kudin Man Fetur N1200 a Maimakon N620 a Gidajen Mai
- Kamfanin NNPCL ya fitar da jawabi a matsayin raddi ga masu jita-jita ana shirin yin karin kudin fetur
- Olufemi Soneye ya musanya labarin, ya kuma ce an daina biyan tallafin man fetur gaba daya a Najeriya
- Jami’in na NNPC Ltd ya ce jama’a su yi watsi da maganar tashin farashi, kuma akwai isasshen mai
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Kamfanin NNPCL wanda shi ne ke kula da harkar mai a Najeriya, ya jaddada cewa an yi waje da tallafin fetur.
A wani jawabi na musamman da kamfanin ya fitar a X a ranar Laraba, ya yi watsi da wani rade-radin da yake yawo.
Rade-radin tashin kudin fetur
Jita-jita sun yada ko ina cewa akwai yiwuwar farashin man fetur ya tashi daga yadda aka saba saye zuwa N1, 200.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL ya musanya wannan batu, ya ce ba rage tallafin man fetur aka yi ba, an yi watsi da tsarin ne gaba dayansa.
Tribune ta rahoto kamfanin man na kasa watau NNPCL ya nuna babu abin da gwamnati ta ke biyan ‘yan kasuwa.
Kwanaki an ji yanzu kusan kamfanin NNPCL kadai ke iya shigo da mai Najeriya.
NNPC ya ce fetur bai tashi ba
Mista Olufemi Soneye ya fitar da jawabi a dandalin X a jiya a matsayin babban jami’in sadarwa na kamfanin NNPC Ltd.
NNPC Ltd ya jaddada bai samu sabani da kowane bangare ba, akasin rahoton da aka fitar a safiyar ranar Larabar nan.
Jawabin ya ce kanun labarin abin tir ne, an nemi tabbatar da zargin rage tallafin wanda NNPC ya ce an janye gaba daya.
Fetur: Jawabin kamfanin NNPCL
"Babu shirin kara kudin man fetur, NNPC Ltd ya tabbatarwa ‘yan Najeriya
Kamfanin mai na kasa (NNPC) Ltd. yana mai tabbatarwa al’umma cewa babu shirin karin farashin PMS, aka fi sani da fetur.
NNPC Ltd yana kira ga ‘yan Najeriya su yi watsi da rade-radin tashin farashin man fetur.
Ana bada shawara ga masu abin hawa a fadin kasar nan su guji sayen man da ba su bukata domin akwai fetur a kasar."
- Olufemi Soneye
Nawa ne gaskiyar kudin fetur?
Rahoto ya zo cewa ana zargin yadda Dala ta tashi da kuma lura da tsadar danyen mai, ya kamata farashin fetur ya tashi.
Masanan bankin duniya sun yi mamakin ganin an shafe wata da watanni ba a samu canjin farashi mai yawa a kasar ba.
Asali: Legit.ng