Almundahar N37bn: Ministan Gwamnatin Buhari Sadiya Farouq Ta Yi Biris Da Gayyatar EFCC

Almundahar N37bn: Ministan Gwamnatin Buhari Sadiya Farouq Ta Yi Biris Da Gayyatar EFCC

  • Sadiya Farouq, tsohuwar minista, ta ki amsa gayatar da Hukumar yaki da rashawa (EFCC) ta yi mata
  • Legit Hausa ta fahimci cewa hukumar ta EFCC na bincike ne kan zargin almundahar naira biliyan 37 da aka ce an yi a zamanin Farouq ta hannun wani dan kwangila, James Okwete
  • Majiya daga hukumar EFCC, kamar yadda aka rahoto ta tabbatar cewa Sadiya ta yi biris da gayyatar da hukumar ta mata a ranar Laraba, 3 ga watan Janairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Tsohuwar ministan jin-kai, Sadiya Umar Farouq, a ranar Laraba, ta ki amsa gayyatar da Hukumar yaki da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta mata bisa binciken zargin halasta kudin haram da ya kai naira biliyan 37 a lokacin tana rike da mukami.

Kara karanta wannan

Mummunan hatsari ya lakume rayukan akalla mutum 6 a babban titin Kaduna zuwa Zariya

Rahotanni sun nuna cewa an karkatar da wannan kudi ne ta hannun wani dan kwangila mai suna James Okwete kamar yadda jaridar Punch ta wallafa.

Sadiya Farouq ta yi biris da gayyatar EFCC
Sadiya Farouq ta ki amsa gayyatar da EFCC ta mata. Hoto: Sadiya Farouq
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gayyaci tsohuwar ministan ta bayyana gaban masu bincike a hedkwatar EFCC da ke Jabi Abuja misalin karfe 10 na safiyar Laraba, 3 ga watan Janairun 2024, don bada ba'asi kan zargin almundahar da aka yi a lokacin tana ofis.

Sadiya Farouq ba ta amsa gayyatar EFCC ba

Amma, wakilin The Punch wanda ya kasance a hedkwatar na EFCC daga karfe 9 na safiya har zuwa 6.30 na yamma ya tabbatar tsohuwar ministan ba ta taho ofishin hukumar yaki da rashawar ba don amsa tambayoyi.

Wani cikin masu tambayoyin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tawagar masu tambayoyin sun tashi aiki misalin karfe 6 na yamma lokacin da suka tabbatar tsohuwar ministan ba za ta zo ba.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Tinubu ya dakatar da Halima Shehu watanni bayan nada ta a matsayin shugabar NSIPA

"Yanzu muka tashi aiki saboda ba ta zo ba yau, har karfe 6 na yamma ya yi. Tabbas ba za ta zo yau ba," a cewar majiyar.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164