Allah Sarki: An Samu Asarar Rayukan Bayin Allah a Wani Mummunan Hatsarin Mota
- An samu asarar rayukan mutum 11 a wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da wasu motoci biyu a jihar Kwara
- Hatsarin motan dai ya auku ne bayan wata motar bas ɗauke da fasinjoji ta wuce wata mota bisa kuskure inda ta yi karo da wata babbar mota mai tahowa
- Mutum bakwai ne suka samu raunuka daban-daban a hatsarin inda aka garzaya da su zuwa asibiti domin duba lafiyarsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi.
Jihar Kwara - Wani hatsarin mota ya rutsa da wata babbar mota da wata motar bas mai ɗauke da fasinjoji 18 a kan hanyar Jebba zuwa Ilorin a jihar Kwara.
Hatsarin wanda ya auku a ranar Talata, 2 ga watan Janairun 2024, ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutum 11.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa wasu mutum bakwai sun samu raunuka daban-daban a hatsarin, wanda ya faru da misalin ƙarfe 4:50 na safe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hatsarin dai ya faru ne a lokacin da wata motar fasinja wacce ta taso daga Gombe ta yi yunƙurin wuce wata motar, lamarin da ya yi sanadin yin karo da wata babbar motar da ke tahowa.
Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa an kai waɗanda suka jikkata a hatsarin zuwa asibitin Ife Oluwa da ke Bode-Saadu, hedikwatar ƙaramar hukumar Moro a jihar, domin duba lafiyarsu, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Me hukumomi suka ce kan hatsarin?
Basambo Busari, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC), reshen jihar Kwara, ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma adadin waɗanda suka mutu a wata sanarwa a ranar Talata.
A kalamansa:
“A ranar Talata, 2 ga watan Janairu, 2024, wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da motoci biyu, Motar DAF da wata motar bas ƙirar Toyota Hiace a Aiyere dake kan hanyar Bode-Saadu-Ilorin.
"Bincike na farko ya nuna cewa motar Toyota Hiace da ta taso daga Gombe zuwa Legas ta wuce wata mota bisa kuskure, wanda hakan ya yi sanadiyyar karo da wata motar DAF da ke tahowa.
"Mutum 18 ne hatsarin ya ritsa da su, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 11, yayin da sauran mutum bakwai suka samu raunuka daban-daban. An kubutar da su kuma an kai su asibitin Ifeoluwa Bode-Saadu, inda a yanzu haka suke jinya."
Mutum 6 Sun Rasu a Hatsarin Mota
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu asarar rayukan mutum shida a wani mummunan hatsarin mota da ya auku kan babban titin Kaduna zuwa Zariya.
Hatsarin dai ya auku ne bayan wata mota ƙirar Toyota ta ƙwace sakamakon matsanancin gudun da take yi.
Asali: Legit.ng