Dangote Ya Samu Sabon Matsayi Bayan Attajirin Afirika Ta Kudu Ya Zama Wanda Yafi Kowa Kudi a Afirika
- Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Najeriya, Aliko Dangote, yanzu ya zama mutum na biyu mafi arziƙi a Afirika a cewar mujallar Forbes
- Dangote ya biyo bayan hamshaƙin attajirin Afirika ta Kudu Johann Rupert, wanda shi ne shugaban kamfanin kayayyakin alatu na Swiss Compagnie Financière Richemont
- Ana sa ran Dangote zai ƙara samun arziƙi a shekarar 2024 yayin da matatarsa ta fara samarwa da sayar da kayayyakinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Hamshakin attajirin nan ɗan ƙasar Afirika ta Kudu Johann Rupert ya fara sabuwar shekara a matsayin wanda ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, inda ya ke gaban Aliko Dangote.
A cewar Forbes, dukiyar da Rupert ya samu ya zuwa ranar Talata 2 ga watan Janairun 2024, ta kai dala biliyan 10.3, wanda ya haura dala biliyan 9.5 na Dangote.
Adadin dukiyar attajirin da ya fi kowa kuɗi a Najeriya a halin yanzu shi ne mafi ƙaranci, na adadin da ya fara sabuwar shekara da shi a cikin shekara 10 da suka gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Forbes yanzu ta bayyana Dangote a matsayi na 230 a jerin attajirai a duniya sai Rupert yana a matsayi na 192.
Yanzu dai Dangote ya zama na biyu
Dangote ya shafe shekaru 12 yana matsayi na ɗaya a jerin Forbes, inda a shekarar 2014 ya samu matsayi mafi girma a lokacin da dukiyarsa ta haura dala biliyan 20.
A tsawon shekaru, arziƙin Dangote ya ragu daga dala biliyan 25 a shekarar 2014 zuwa dala biliyan 9.5 a halin yanzu, musamman saboda faɗuwar darajar kuɗin Najeriya.
Dangote ya cigaba da riƙe matsayi na farko a Bloomberg
Duk da haka, a cikin jerin hamshaƙan attajirai na Bloomberg, Dangote ya cigaba da kasancewa a matsayi na farko na wanda ya fi kowa arziƙi a Afirika.
Jerin ya nuna Dangote a matsayi na 128 a jerin attajirai na duniya, inda yake da arziƙin da ya kai dala biliyan 15.1.
Wannan ya zarce na Rupert, wanda ke matsayi na 162 da dukiyar da ta kai dala biliyan 12.4.
Dangote Zai Sayar da Jirginsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa hamshaƙin attajirin nan Alhaji Aliko Dangote, ya shirya sayar da katafaren jirginsa na alfarma ƙirar Bombardier Global Express XRS.
Dangote ya biya dala miliyan 45.5 don mallakar jirgin mai zaman kansa a shekarar 2009 lokacin da yake bikin cika shekaru 53 da haihuwa a duniya.
Asali: Legit.ng