Yanzun Nan: Tinubu Ya Dakatar da Halima Shehu Watanni Bayan Nada Ta a Matsayin Shugabar NSIPA
- An sauke Halima Shehu, shugabar hukumar NSIPA mai kula da jin dadin al'umma daga mukaminta
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dakatarwar wanda aka sanar a yayin wani shirin kai tsaye a ranar Talata, 2 ga watan Janairu
- Har yanzu ba a tantance musabbabin dakatar da ita ba, duba da ganin cewa yan watanni da suka gabata ne aka daura ta kan mukamin
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da dakatar da Halima Shehu a matsayin shugabar Hukumar Jin Dadin Al'umma ta Kasa (NSIPA).
Channels TV ce ta sanar da hakan a ranar Talata, 2 ga watan Janairu, a daya daga cikin shirye-shiryenta, 'The Morning Brief'.
Kafar yada labaran ta kuma bayyana cewa nan take shugaban kasar ya amince da dakatar da Shehu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Nigerian Tribune ta rahoto, matakin na zuwa ne watanni uku bayan majalisar dattawa ta tabbatar da ita kan kujerar.
Bayanin Halima Shehu
Shehu, Kwararriya a bangaren hada-hadar kudi, ta rike matakan shugabanci a bangarori dagban-daban a fadin bakuna uku, bangaren kula da kudi, aika kudi, tantancewa, ayyuka da sauransu.
Ta koma bangaren siyasa ne a shekarar 2010 sannan ta yi aiki a matsayin babbar mataimakiya ta musamman ga tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shema a shekarar 2011.
Ta kuma ba da gudunmawarta a matsayinta na ma’aikaciyar hukumar tara haraji ta jiha.
A 2016, Shehu ta fadada tunaninta ta hanyar karbar mukamin wucin gadi a matsayin mai sa ido kan zaben shugaban kasa a Cape Verde a karkashin kungiyar ECOWAS.
Bayan nan, daga 2017 zuwa 2022, ta kai kwarewarta Ma'aikatar Jin kai da walwalar jama'a ta tarayya.
Tinubu yana shirin maye gurbin Lalong
A wani labarin kuma, mun ji cewa shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya fara neman shawarwari kan wanda ya kamata ya maye gurbin Simon Lalong a matsayin ministan kwadago da samar da ayyukan yi.
A rahoton Bussines Day, Shugaba Tinubu ya gana da Lai Muhammed, tsohon ministan yaɗa labarai da al'adu a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari.
Bayan haka, Shugaban kasar ya kuma gana da tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.
Asali: Legit.ng