Bola Tinubu: Fitaccen Malamin Addini Ya Bayyana Abu 1 da Ba Zai Yi Tasiri ba a 2024
- Babban faston Najeriya, Rev James Odedeji ya yi hasashen cewa ba za a samu shugabanci wanda yake ba nagari ba a Najeriya a 2024
- Malamin addinin ya kuma yi addu'ar cewa 2024 za ta zama shekarar da Najeriya za ta ci gaba kuma yan Najeriya za su ga daukakar da Allah ya yi wa kasar nan
- Sakon Odedeji na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban kasa Tinubu ya rattaba hannu a kasafin kudin da ya ya yi wa lakabi da na sabonta fata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Lagos - Rt Rev James Odedeji, babban faston cocin 'Diocese of Lagos West of the Anglican Communion', ya yi addu'ar cewa yan Najeriya ba za su fuskanci lalataccen shugabanci ba a 2024.
Sabuwar shekara: "Dala za ta kai N2,500", Babban malamin addini ya hango abun da zai faru a Najeriya
A sakonsa na sabuwar shekara, malamin addinin ya ce yana da yakini mai kyau game da makomar Najeriya kuma cewa an yi alkawarin sabuwar shekara za ta zama shekara mai ban mamaki ga kasar, rahoton Punch.
Wannan sakon yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da jagoran tawagar yada labarai na Diocese, Tunji Oguntuase, ya fitar a ranar Litinin, 1 ga watan Janairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bishop Odedeji yayi addu’ar samun shugabanci na gari a Najeriya
Odedeji ya yi wa Najeriya da cibiyoyin gwamnati addu'a a cikin sakonsa, inda ya kara da cewa lokaci ya yi da za a fifita Najeriya.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya sa Najeriya ta sha kan dukkanin sharri, sannan cewa yan Najeriya za su rayu domin shaida sabbin abubuwan da Allah ya tsara wa kasar.
Malamin addinin ya ce:
"Duk abubuwan da ke haifar da mummunan shugabanci ba za yi tasiri ba a wannan shekarar. Ina da yakinin cewa Najeriya za ta fuskanci sabon rayuwa duk da munanan kalubalen da ke fuskantarmu."
Bishop ya bukaci yan siyasa da su gyara zama yayin da Tinubu ya rattaba hannu a kasafin kudin 2024
Malamin addinin ya kuma bukaci wadanda ke rike da mulki a kasar da su koma bakin aiki.
Sakon Odedeji na zuwa ne a farkon shekara lokacin da Shugaban kasa Bola Tinubu zai aiwatar da kasafin kudinsa na farko, wanda ya yi wa lakabi da "kasafin kudin sabonta fata" a lokacin da yan Najeriya ke kukan tsadar rayuwa tun bayan da ya hau karagar mulki.
Haka kuma a wannan rana ne shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin kasafin kudin.
Malami ya yi hasashe kan 2024
A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa Bishop Joseph Edoro,o kuma babban fasto kuma wanda ya kafa majami'ar 'A Touch From Heaven International Ministry', ya magantu a kan shekarar 2024 mai zuwa yayin da shekarar 2023 ta zo karshe.
A wata hira da jaridar Independent, malamin addinin ya magantu kan abun da Ubangiji ya nuna masa, yana mai cewa yan Najeriya su yi tsammanin ganin manyan coci sun rarrabu zuwa kanana.
Asali: Legit.ng