“Sun Ce Zai Kammalu a Disamba”: Iyali Sun Kadu Bayan Ganin Katafaren Gidansu a Kauye

“Sun Ce Zai Kammalu a Disamba”: Iyali Sun Kadu Bayan Ganin Katafaren Gidansu a Kauye

  • Wasu iyali a Najeriya sun ce mai kula da aikin ginin gidansu ya sanar da su cewa zai kammalu zuwa watan Disamba
  • Iyalin sun ziyarci ginin a kauyen a lokacin bikin Kirsimeti cike da manyan buruka amma sai suka sha kunya
  • Ejiofor Chibueze Charles, wani kwararren a aikin gini kuma shugaban kamfanin Modern Alternative Design Architects (MAD), ya caccaki dan uwan iyalin kan yanayin da ginin ke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata budurwa yar Najeriya ta ba da labarin abun da iyalinta suka gano a katafaren gidansu na kauye, wanda ya kamata ace an kammala shi.

Dalibar mai karatun likitanci, Nini Ogele, ta yada bidiyon a TikTok kuma ya haifar da cece-kuce a tsakanin masu amfani da dandalin na soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu: Fitaccen Malamin Addini Ya Bayyana Abu 1 da Ba Zai Yi Tasiri ba a 2024

Sun tarar ginin bai kammalu ba
“Sun Ce Zai Kammalu a Disamba”: Iyali Sun Kadu Bayan Ganin Katafaren Gidansu a Kauye Hoto: @niniogele
Asali: TikTok

Sun yi tsammanin ganin katafaren gida da aka kammala amma sai suka tarar da kangon gini. Bidiyon ya nuno iyalin suna zagaya gidan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alamu sun nuna aiki ya fara a ciki, kuma wasu dakuna na dauke da tayil. A cewar matashiyar, sun ji a jikinsu cewa za su sha kunya.

"Ina tunanin gaba dayanmu mun ji a jikinmu cewa ba zai kammalu ba zuwa yanzu," ta yi wa bidiyon take.

Ta ce kawunsu ne yake kula da ragamar aikin ginin.

Kwararre a harkar gini ya daura laifin kan kawunsu

Da yake bayyana ra'ayinsa game da batun kwararre a harkar gini Ejiofor Chibueze Charles ya daura laifin yanayin da gidan ke ciki a kan kawunsu.

A wata hira da jaridar Legit, shugaban kamfanin Modern Alternative Design Architects ya bayyana dalili:

"Duba ga yanayin abubuwa na daura laifin kan dan uwansu (kawu) wanda aka ce ke kula da ginin.

Kara karanta wannan

Abba ko Gawuna? An hango wanda zai yi nasara a kotun koli duba da wasu dalilaia

"An ba shi aikin a kan amana kuma da kamata ya yi ace ya girmama mutanensa ta hanyar tabbatar da cewa babu wata matsala da ta fito da kuma kammalawa lokacin da ake tsammani.
"Idan da akwai dan kwangila kuma bai yi yadda ake tsammani ba, da an yi masa korafi da saita shi, amma idan kawun ne ya yi kokarin cin dunduniyar jama'arsa ya kamata yan uwansa su kai kararsa.
"A karshe an saba yarjejeniyar aiki.
"Ya kamata su duba kudaden da aka tura sannan su duba da aikin da aka yi don sanin ko darajarsa ya kai aikin ko an damfare su ne sannan su san mataki da yawan damfarar da aka yi masu."

Kalli bidiyon a kasa:

Bidiyon ya haifar da martani

grader ya ce:

"Saboda babu wani a wurin don kula da aikin ne."

Petra Louis ta ce:

"Ni da mijina ne wannan yallabai ya kusa kuka, ya yi wa injiniyan duka sannan ya rufe shi."

Kara karanta wannan

"Ya hadu": Wani mai zanen gida ya kafa tarihi, ya gina zagayayyen gida a kauyensa

Michelle ta ce:

"Yarinya irin haka ce ta faru da mu muma."

African beauty ta ce:

"Sun ce Disamba shin sun fada maku Disamba 2023."

Matashi ya mallaki gida a turai

A wani labarin, mun ji cewa wani matashin mutum da ya dauki kasadar zuwa kasar Canada neman aikin yi ya cimma nasara a karshe.

Mutumin ya nunawa mutane sabon gidan da ya siya daga aikin wanke bandaki a kasar Canada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng