Mai Sarautar Gargajiya a Najeriya Ya Kafa Tarihin Duniya Bayan Shafe Awa 120 Ya Na Kallon Talabijin

Mai Sarautar Gargajiya a Najeriya Ya Kafa Tarihin Duniya Bayan Shafe Awa 120 Ya Na Kallon Talabijin

  • Cif Sanya Atofarati ya kafa tarihin zama wanda ya fi kowa dade wa ya na kallon talabijin a duniya
  • Sanya ya shafe awanni 120 ya na kallon talabijin din wanda ya karya tarihin dan kasar Amurka da ya yi awanni 90
  • Sanya ya ce ya na da tabbacin samun satifiket daga kamfanin kundin bajinta na Guinness bayan kammala tantance wa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ekiti - Mai sarautar gargajiya a jihar Ekiti, Cif Sanya Atofarati ya kafa tarihi a kundin bajinta na Guinness, cewar Tribune.

Sanya ya shafe awanni 120 ya na kallon talabijin wanda ya kafa tarihi a matsayin wanda ya fi kowa dade wa a tarihin kamfanin.

Kara karanta wannan

Yayin da ake shan daka a Najeriya, Buhari ya bayyana dalilin farin ciki da ya yi bayan cire tallafi

Basarake ya kafa tarihin zama wanda yafi kowa dadewa ya na kallon talabijin
Mai Sarautar Gargajiya Ya Kafa Tarihi a Kundin Bajinta Na Guinness. Hoto: Sanya Atofarati, GWR.
Asali: Facebook

Yaushe Cif Sanya ya kafa tarihi?

Atofarati ya fara kallon ne a ranar Laraba 27 ga watan Disamba inda ya gama a yau Litinin 1 ga watan Janairu a Ado-Ekiti da ke jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya dauki hankulan mutane a yankin wadanda suka hada da matasa da mata da kuma manya inda suke murna.

Mai saurautar gargajiyar ya ce ya dauki aniyar karya tarihin awanni 90 da wani dan birnin New York na Amurka, Fragoso ya kafa.

Fragoso ya na rike da kambun tun 2016 ba tare da wani ya kusanci karya tarihin ba, cewar The Nation.

Mene Cif Sanya ke cewa?

Sai dai Cif Sanya ya bayyana cewa ya na sa ran samun satifiket kan kafa tarihin da ya yi bayan an kammala tantance shi.

Ya ce:

Muna sa ran karbar yarjewar kamfanin Guinness bayan bin dukkan ka'idojin da suka dace kuma aka gindaya."

Kara karanta wannan

Kano: Dan Majalisar NNPP ya sha suka bayan kaddamar da shiri da 'yan mazabar suka bayyana abin kunya

Atofarati ya godewa 'yan Najeriya da irin goyon baya da suka nuna masa a tsawon wannan lokaci da suke ciki.

Dan Najeriya ya fara kuka don kafa tarihi

A wani labarin, Wani matashi dan Najeriya ya bayyana cewa kundin bajinta na Guinness ya lamunce masa fara gasar kuka na tsawon awanni 200.

Matashin mai suna Oluwatobi Kufeji Àlejòpàtàkì ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar 10 ga watan Yuni cewa ya samu sahalewarsu.

Wannan na zuwa ne bayan matasa da dama sun fantsama cikin gasar tun bayan kafa tarihi da Hilda Baci ta yi a matsayin wacce tafi kowa dadewa ta na girki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.