'Dan Sarkin Kano Ya Bada Mamaki, Ya Haɗu Fitaccen Sarki a Najeriya Sun Je Coci Taron Addu'o'i
- Yariman Kano, ɗan Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya halarci taron addu'ar maraba da sabuwar shekara a Benin
- Masarautar Sarkin Benin a jihar Edo ce ta tabbatar da haka a wata sanarwa, ta ce ganin Musulmi a wurin ya ƙayatar da masu ibada
- Wannan ne karo na farko da irin haka ta auku a cocin da ke Benin, kuma limami ya ja addu'ar har zuwa sabuwar shekara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benin City, jihar Edo - Yarima Isah Ado-Bayero, dan Sarkin Kano, Mai Martaba, Alhaji Aminu Ado-Bayero ya bi sahun Sarkin Benin, Oba Ewure II, wajen gudanar da addu'a a coci.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Yariman Kano da Sarkin Benin sun halarci taron Crossover, wanda ake gudanar da addu'ar tarban sabuwar shekara 2024.
Shari'ar Kano: Mata sun yi gangami don nuna goyon baya ga Abba Gida-Gida gabanin hukuncin Kotun Koli
Fitaccen basaraken ya halarci taron addu'o'in sabuwar shekarar ne a cocin Holy Aruosa Cathedral da ke birnin Benin a jihar Edo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan kuma na zuwa ne bayan Sarkin ya je wannan cocin ranar Lahadi, 31 ga watan Disamba, 2023 domin halartar bikin al'ada na gargajiya 'Igue festival'.
Wannan dai shi ne karo na farko a tarihi da aka samu wani Oba na Benin ya halarci wannam zaman coci.
Ɗan sarkin Kano musulmi ya je coci a Benin
A wata sanarwa da sakataren watsa labaran sarkin Benin ya fitar, ya ce wannan karon, cocin ta karɓi bakuncin wanda ba a saba gani ba, Yarima Isah Ado-Bayero, ɗan Sarkin Kano.
Osaigbovo Iguobaro, ya ƙara da cewa ganin Musulmi wanda ke bin kalandar Hijira ta addinin musulunci ya ƙayatar da masu ibada a cocin Holy Aruosa wacce aka fi sani da Cocin Edo ta ƙasa.
Shugaban limaman cocin Holy Aruosa Cathedral, Ohen-Osa Igbinoghodua Edebiri, shi ne ya jagoranci taron addu’o’in da ya kai masu ibada shiga sabuwar shekara.
APC ta fara farfaɗowa a jihar Ribas
A wani rahoton na daban Jam'iyyar APC ta ayyana shirin da take na karɓe ragamar mulkin jihar Ribas daga hannun jam'iyyar PDP a babban zaben 2027.
Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ta jihar, Chief Tony Okocha ne ya faɗi haka a Patakwal, babban birnin jihar.
Asali: Legit.ng