Hukumar Hajji ta Zamfara ta mayar da naira miliyan 747 ga maniyyata 504

Hukumar Hajji ta Zamfara ta mayar da naira miliyan 747 ga maniyyata 504

Hukumar aikin Hajji ta jihar Zamfara ta fara mayar da naira miliyan 747 ga maniyyata 504 da suka fara tara kudin tun daga 2019 zuwa 2023.

Shugaban hukumar, Musa Mallaha, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a Gusau ranar Asabar.

An dawowa maniyyata a Zamfara kudinsu
Hukumar Hajji ta Zamfara ta mayar da naira miliyan 747 ga maniyyata 504 da suka biya a baya. Hoto: @daily_trust
Asali: Facebook

Ya ce Gwamna Dauda Lawal ya amince da fitar da naira miliyan 218 duk wata don biyan kudin a hankali daga Disamba zuwa Fabrairu, Daily Nigerian ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Mallaha ya ce hukumar za ta sa naira miliyan 92 kari kan kudin da gwamnan ya amince a mayar.

"Gwamna ya amince da mayar da naira miliyan 747 ga wanda abin ya shafa cikin biya uku tsakanin Disambar 2023 zuwa Fabrairun 2024.

Kara karanta wannan

"Manyan coci za su ruguje": Malamin addini ya yi hasashe kan 2024, ya jero masifu 4 a mulkin Tinubu

"Zancen da na ke yanzu, gwamna ya biya naira miliyan 218 na watan Disamba don biyan kaso na farko.
"Tuni an tura kudin zuwa asusun hukumar Hajji", in ji shi

Ya ce kudin zai zama kari kan naira miliyan 92 da ke asusun hukumar kafin fara rabawa wanda za su ci gajiyar.

"Za mu fi mayar da hankali ga wanda su ka nuna sha'awar zuwa hajjin 2024, musamman wanda suka ajiye wani kudi a hukumar", in ji Malam Mallaha.

Shugaban hukumar ya yi alkawarin yin aiki da gaskiya ya yi gudanar da aikin, ya kuma yaba wa gwamnan bisa yadda ya bai wa hukumar kula

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164