“Manyan Coci Za Su Ruguje”: Malamin Addini Ya Yi Hasashe Kan 2024, Ya Jero Masifu 4 a Mulkin Tinubu
- Gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ta samu hasashe mara dadi gabannin 2024 yayin da Bishop Joseph Edoro ya bayyana abubuwa hudu da za su faru a sabuwar shekarar
- Edoro, wanda ya kafa majami'ar 'A Touch From Heaven International Ministry', ya ce Allah ya albarkaci Najeriya a 2024 amma shugabanni sun karkatar da makomar kasar
- Malamin addinin ya ce manyan coci za su wargaje zuwa kanana sannan Shugaban kasa Tinubu zai kafa manufofi da ba za su yi wa mutane dadi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Ifako-Ijaye, Lagos - Bishop Joseph Edoro,o kuma babban fasto kuma wanda ya kafa majami'ar 'A Touch From Heaven International Ministry', ya magantu a kan shekarar 2024 mai zuwa yayin da shekarar 2023 ta zo karshe.
A wata hira da jaridar Independent, malamin addinin ya magantu kan abun da Ubangiji ya nuna masa, yana mai cewa yan Najeriya su yi tsammanin ganin manyan coci sun rarrabu zuwa kanana.
Haka kuma, ya bayyana cewa Shugaban kasa Bola Tinubu zai kafa manufofin da ba za su yi wa mutane dadi ba wanda zai haifar da rikici.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin addinin ya jaddada cewar 2023 shekara ce mai cike da radadi, amma Allah ya albarkaci yan Najeriya da juriya da kamun kai.
A cewarsa, abin al’ajabi da ya faru a shekarar 2023 shi ne yadda Najeriya ta tsira. Ya ce shekarar ta yi amfani kamar yadda ake tsammani, amma shugabannin sun lalata makomar kasar.
Hasashen 2024 game da Shugaban kasa Bola Tinubu
Da yake magana game da 2024, malamin ya ce:
Farashin mai zai zube gaba daya, malamin addini ya yi hasashen shekarar 2024, ya fadi sauran abubuwa
- Za a samu karin tashin hankalin siyasa da na kwadago. Gwamnati mai ci za ta nemi mayar da Najeriya kasa mai jam’iyya daya.
- Wata tukunya za ta dauko tafasa daga Arewa, sannan ta tsiyaye kanta a Kudu. Manyan coci za su ruguje sannan su wargaje zuwa bangare-bangare.
- Wasu kwararrun runduna ta matasa za su hade don su kafa kungiya, sannan hadin kai mara rushewa zai kaurace kamar walkiya.
- Yunwa za ta karu a kasar. Za a cire tsammani da rahama. Amma, kuma, wadanda suka san Allah za su yi karfi sannan su amfana
Malamin addini ya fadi gwamnan Ondo a 2024
A wani labarin kuma, mun ji cewa babban faston da ke jan ragamar cocin Dominion Faith, Ore, Ondo, Prophet Ifetayo Afinjuomo, ya ce wani dan siyasa daga yankin karamar hukumar Ile Oluji/Okeigbo na jihar, shine zai lashe zaben gwamnan jihar Ondo a 2024.
Bai dade ba da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta sanar da ranar zaben gwamna a jihar Ondo.
Asali: Legit.ng