Hukumar Yan Sanda Ta Bayyana Abun da Zai Faru da Jami’an da Aka Gani Suna Tsintar Kudin da Aka Watsa
- Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana abun da za a yi wa jami'an da aka gani a wani bidiyo da ya yadu suna tsintar kudi a kasa a filin jirgin sama na Benin
- Kakakin hukumar yan sandan, Olumuyiwa Adejobi ya ce za a zaunar da jami'an yan sandan a wayar masu da kai kan yadda za su kaurace wa irin wannan abu a nan gaba
- Adejobi ya ce an dauki abun da suka aikata a matsayin karamin laifi kuma ba zai sa a kore su ba
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Benin, Jihar Edo - Hukumar yan sandan Najeriya ta yi martani a kan wani bidiyo da ya yadu, na jami'ai da aka gani suna tsintar kudin da mawaki, Shallipopi ya watsa a kasa a filin jirgin sama na Benin, jihar Edo.
Apapa: Sabon rikici ya ɓalle a jam'iyyar adawa yayin da aka lakaɗa wa wasu jiga-jigai 2 dukan kawo wuƙa
Kakakun hukumar yan sandan, Olumuyiwa Adejobi, ya ce ba za a kori jami'an yan sandan ba, rahoton Punch.
Adejobi ya ce an dauki abun da suka aikata a matsayin karamin laifi da ba zai kai ga sallamarsu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa za a wayar masu da kai kan yadda za su kaurace wa irin wannan abu a gaba.
Ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 29 ga watan Disamba, yayin da yake martani ga fargabar jama'a cewa watakila a kori jami'an tsaron daga aiki.
An hasko jami'an a cikin wani bidiyo da ya yadu suna tsintar kudi da mawaki Shallopopi ya dungi jefawa a sama a filin jirgin sama na Benin.
Da yake martani ga bidiyon a Instagram, Adejobi ya ce:
"Ba za mu kori wani dan sanda don ya tsinta irin wannan kudi ba, kawai dai za mu wayar masa da kai cewa kada ya sake yin irin haka, domin wannan yana mayar da shi baya."
Wani mai amfani da dandalin X, @Wizillden, ya wallafa bidiyon a shafinsa a ranar Juma'a, 29 ga watan Disamba.
Bidiyon yar sanda taka rera taken kasa
A wani labarin, mun ji cewa masu kallo da dama sun girgiza yayin da wata jami'ar yar sanda ta rera wakar taken kasar cike da kura-kurai a wani taron manyan jami'an yan sanda a Owerri, jihar Imo.
Bidiyon jami'ar yar sandar tana tsallake wasu baitoci wajen rera taken kasar ya yadu a dandalin soshiyal midiya.
Asali: Legit.ng