"Muna Daukar Mataki": Gwamnatin Bayelsa Ta Yi Martani Kan Auren Yar Shekara 4 da Dan Shekara 54

"Muna Daukar Mataki": Gwamnatin Bayelsa Ta Yi Martani Kan Auren Yar Shekara 4 da Dan Shekara 54

  • Auren da aka kulla tsakanin yarinya yar shekara hudu da tsoho dan shekara 54 a garin Akeddei ya ja hankalin gwamnatin jihar Bayelsa
  • Gwamnatin da Gwamna Douye Diri ke jagoranta ta tsoma baki ta hanyar gayyatar iyayen yarinyar da mijin nata
  • Gwamnatin jihar ta ce tana daukar matakin ceto yarinyar daga wajen dukkanin masu hannu a wannan haramtaccen biki

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Bayelsa , Akeddei - Gwamnatin jihar Bayelsa ta sanya baki a haramtaccen auren da aka yi wa wata yarinya yar shekara hudu da wani dattijo dan shekara 54 a garin Akeddei, karamar hukumar Sagbama ta jihar.

Gwamnatin Gwamna Douye Diri ta gayyaci iyayen karamar yarinyar da kuma mutumin mai shekara 54 bayan auren ya yadu a shafukan soshiyal midiya, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Katsina ta dakatar da jami’i kan sayar da gandun daji

Gwamnatin Bayelsa ta magantu kan auren yar shekara 4 da dattijo
"Muna Daukar Mataki": Gwamnatin Bayelsa Ta Yi Martani Kan Auren Yar Shekara 4 da Dan Shekara 54 Hoto: Douye Diri
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da ma’aikatar harkokin mata, yara da ci gaban al’umma ta saki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin jihar mai albarkatun man fetur ta ce auren ya saba wa adalci, daidaito da kuma sanin yakamata.

A cewar jaridar New Telegraph, basaraken ya amsa gayyatar da gwamnati ta yi masa, kuma ya yi alkawarin gabatar da yarinyar, iyayenta, angon, shugaban matasa da kuma shugaban kwamitin ci gaban al’umma na yankin.

Gwamnatin jihar ta ce bata goyon bayan auren kananan yara da sunan al'ada.

"Wannan ne dalilin da yasa gwamnatin jihar ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen amincewa da dokar kare hakkin yara ta jihar Bayelsa.
"Muna daukar matakai don kubutar da yarinyar daga dukkan masu alaka da wannan haramtaccen biki da suka yi wa lakabi da "al'amari na tsarkakewa kawai."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan gida daya su 8 sun mutu a hatsarin mota yayin zuwa bikin sabuwar shekara

Gwamnatin ta kuma ce tana aiki tare da rundunar yan sandan jihar Bayelsa, don tabbatar da ganin irin haka bai sake faruwa ba a jihar.

Rudani bayan an yi yar shekara 4 aure

A baya mun ji cewa al’ummar kauyen Akeddei da ke karamar hukumar Sagbama a jihar Bayelsa sun shiga rudani bayan aurar da wata yarinya ‘yar shekara 4 ga wani dattijo.

Iyayen yarinyar ne suka ba da auren yarinyar wacce ba a bayyana sunanta ba ga dattijo dan shekara 54 wanda hakan ya jawo cece-kuce a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng