"Muna Jin Yunwa": Yan Legas Sun Gaya Wa Tinubu Gaskiyar Halin da Ake Ciki a Kasa a Wani Bidiyo
- Mazauna Legas sun bayyana kokensu ga shugaban ƙasa Bola Tinubu, inda suka yi ta kururuwa "muna jin yunwa" a harshen Yarbanci a lokacin da ayarinsa ke wucewa
- Tinubu wanda ke Legas domin hutu, ya halarci Sallar Juma’a a babban Masallacin Legas, a ranar Juma’a, 29 ga watan Disamba
- Ƴan Najeriya a shafukan sada zumunta sun mayar da martani, inda wasu ke bayyana halin ƙuncin rayuwa, wasu kuma na nuna shakku kan tsaftar Legas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Legas, Najeriya - Wasu mazauna jihar Legas a ranar Juma'a, 29 ga watan Disamba, sun bayyana kokensu ga shugaban ƙasa Bola Tinubu, inda suka yi ta ihun "muna jin yunwa" a harshen Yarbanci yayin da ayarinsa ke wucewa.
Shugaba Tinubu, wanda ya je Legas domin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara, ya ziyarci babban masallacin Legas da ke tsibirin Legas, domin yin Sallar Juma’a a ranar Juma’a.
Yayin da ayarin motocin nasa ke hanyar zuwa masallacin, wasu mazauna garin da aka ji muryoyinsu a cikin wani faifan bidiyo na X sun yi ta kururuwa cikin harshen Yarbanci suna cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ebi npa wa oo, Asiwaju (muna jin yunwa, Asiwaju)"
Ƴan Najeriya na bukukuwa ƙarshen shekara cikin jerin ƙalubalen tattalin arziƙi da suka haɗa da hauhawar farashin kayayyaki, ƙarin farashin man fetur da kuma ƙarancin kudi.
A cikin wani bidiyo, reshen jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar Birtaniya ya naƙalto wasu sassa na kalaman Tinubu na baya-bayan nan inda ya amince da raɗaɗin da ƴan Najeriya ke ciki.
Rubutun na cewa:
"Ina jin zafin ku, sadaukarwarku ba za ta zama a banza ba" - Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR.
"Najeriya na cikin tsaka mai wuya. Zan yi aiki don ganin an fitar da ƴan Najeriya daga ƙangin talauci. Ku yi aiki tare da ni don yaƙar talauci da ta'addanci."
Ƴan Najeriya sun mayar da martani
@chymaker, ya rubuta:
"Ku duba wurin da ayarinsa suka bi, jama'a na mutuwa saboda yunwa, amma yana rayuwa da bai taɓa mafarki ba da kuɗin ƴan Najeriya."
@PatoEner, ya rubuta:
"Me yasa Legas tayi datti haka?"
@Pauly2570 ya rubuta:
"Wannan shine dalilin da ya sa suke neman mulki ido a rufe. Girman kai da rayuwa cikin jindaɗi da wadata."
@icapcorn, ya rubuta:
"A rayuwata ta gaba, ina so na tashi a cikin ƙasashen Turai. Haihuwa ta a Najeriya kuskure ne."
Abdulsamad Ya Gana da Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu BUA, ya gana da shugaban ƙasa Bola Tinubu a Legas.
Bayan ganawarsu, Abdulsamad ya yi alƙawarin siyar da simintin BUA a kan farashin N3,500.
Asali: Legit.ng