Uwargidan Gidan Shugaban Kasa Remi Tinubu Ta Ziyarci Iyalan Akeredolu, Bayanai Sun Fito
- Uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta ziyarci iyalan marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, wanda ya rasu a ranar 27 ga watan Disamba
- Remi Tinubu, tare da rakiyar mataimakin gwamnan jihar Oyo da wasu manyan baƙi, sun yi ta'aziyyar Akeredolu a gidansa na Jerico dake Ibadan
- A yayin ziyarar, ta bayyana Akeredolu a matsayin babban mutum, tare da miƙa fatan alheri ga cigaban abubuwan da ya bari, tare da yin ta'aziyya ga iyalan da ke cikin baƙin ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Ibadan, jihar Oyo - Uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, a ranar Asabar, 30 ga watan Disamba, ta ziyarci iyalan marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.
Remi Tinubu, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, ta isa gidan Akeredolu dake Jerico da misalin ƙarfe 12:45 na rana tare da mataimakin gwamnan jihar Oyo, Bayo Lawal da wasu manyan baƙi.
Legit.ng ta tattaro cewa uwargidan Akeredolu, Betty Anyanwu-Akeredolu da sauran iyalansa ne suka tarbe uwargidan shugaban ƙasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akeredolu ya rasu ne a ranar Laraba 27 ga watan Disamba yana da shekaru 67 a duniya.
Akeredolu: Najeriya ta yi rashin babban mutum - Remi Tinubu
Da take jawabi yayin ziyarar ta’aziyyar, Remi Tinubu ta ce da rasuwar Akeredolu, Najeriya ta yi rashin babban mutum.
Ta yi nuni da cewa tsohon gwamnan jihar Ondo babban mutum ne kuma za a yi kewarsa sosai.
A Kalamanta:
"Mu kawai za mu yi fatan cewa abin da ya bari ya cigaba kuma ya dawwama. Ina yi wa matarsa da ƴaƴansa da jikokinsa da kuma iyalansa fatan Allah Ya ba su lafiya, Ya kuma rage musu raɗaɗin da suke ciki.
"Ya kamata su rayu tare da sanin gaskiyar cewa ya yi iyakar ƙoƙarinsa, ya kyautata wa mutane, za a yi kewar sa sosai."
Tinubu Ya Yi Ta'aziyyar Akeredolu
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyyar marigayi Rotimi Akeredolu, tsohon gwamnan jihar Ondo.
Shugaba Tinubu ya bayyana Akeredolu a matsayin mutum mara tsoro wanda za a yi kewarsa sosai.
Asali: Legit.ng