Kano: Gwamna Abba Ya Damƙa Kananan Yara 7 Hannun Iyayensu Bayan Ceto Su, Ya Tura Sako Bauchi

Kano: Gwamna Abba Ya Damƙa Kananan Yara 7 Hannun Iyayensu Bayan Ceto Su, Ya Tura Sako Bauchi

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf da miƙa kananan yaran da dakarun yan sanda suka ceto hannun iyayensu
  • Abba ya gargaɗi iyayen su kara kulawa da taka tsan-tsan domin guje wa bara gurbi da ke ɗauke yara su sayar da su ga wasu mutane
  • Rundunar ƴan sandan Kano ta ceto kananan yara 7 da aka sace daga Bauchi kuma aka siyar da su a jihohin kudu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kono, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya damƙa kananan yara bakwai hannun iyayensu, waɗanda aka sato daga jihar Bauchi.

Vanguard ta ce hakan na kunshe a wata sanarwa da kakakin gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Jumu'a, 29 ga watan Disamba, 2023 a Kano.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka bai wa ma'aikatan jihohinsu kyautar N100,000 a ƙarshen 2023

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.
Gwamna Yusuf Ya Mika Yaran da Aka Sace Hannun Iyayensu a Jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamnan ya nuna matukar bacin ransa game da abinda ya faru har aka sace ƙananan yaran guda bakwai daga Bauchi sannan aka yi safararsu da sayar da su a jihohin Anambra da Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Gida-Gida ya yi mamakin yadda tawagar masu aikata laifin suka ƙware wajen sace ƙananan yara daga jihohin arewa tare da zuwa can wani wuri su sayar da su.

Gwamnan ya jinjinawa rundunar yan sanda

Haka nan kuma gwamnan ya yabawa namijin kokarin rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ƴan sanda, CP Muhammad Hussain Gumel.

A cewarsa, kokarin dakarun ƴan sanda ne ya yi sanadin kama masu safarar kananan yaran tare da ceto waɗannan guda takwas, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya kuma bukaci iyaye da su kasance masu taka-tsan-tsan da kula da lafiyar ‘ya’yansu a matsayin babban nauyin da Allah ya ɗora musu.

Kara karanta wannan

"Tsoron kotun koli": Yan Najeriya sun yi martani bayan gwamnan PDP ya yi wa Tinubu addu'a

Abba ya aike da sako ga Gwamnan jihar Bauchi

Gwamna Abba Kabir ya kuma yi kira ga takwaransa na jihar Bauchi, Bala Muhammed, da ya dauki kwararan matakai na shari’a a kan wadanda ake zargin.

Tun da farko, Malam Saad daga Bauchi, mahaifan daya daga cikin yaran ya ce ya rasa kalmomin da zai amfani da su wajen godiya ga Gwamna da Kwamishinan ‘yan sanda na Kano bisa kokarin ceto ƴaƴansu.

An fara zaman makokin kwanaki 3 a Ekiti

A wani rahoton kuma Gwamna Oyebanji na jihar Ekiti ya ayyana zaman makokin kwanaki uku domin jimamin rasuwar shugaban gwamnonin kudu.

Biodun Oyebanji ya kuma bada umarnin sauke dukkan tutocin gwamnati zuwa rabi domin girmama marigayi Akeredolu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262