Wani Bam da Aka Dasa Ya Tashi, Ya Yi Ajalin Wani Jami'in Hukumar NSCDC a Jihar Arewa
- Wani jami'an hukumar tsaro ta Sibil Defens, Abubakar Nurudeen, ya rasa rayuwarsa bayan taka bam a jihar Borno
- Rahoto ya nuna cewa Nurudeen ya je duba layukan raba wutar lantarki da ƴan ta'adda suka rusa kwatsam ya taka abun fashewar
- Hukumar NSCDC ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tuni aka masa jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanaza
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Borno - Wani abun fashewa (IED) watau bam ya yi sanadin mutuwar wani jami'in hukumar sibil defens (NSCDC), Abubakar Nurudeen, a jihar Borno.
Bam ɗin ya tashi da jami'in tsaro ne a kauyen Jakana, yankin ƙaramar hukumar Konduga a daidai kusa da titin Maiduguri zuwa Damaturu, a jihar Borno.
An ce mamacin na aikin duba layukan wutar lantarki na kamfanin rarraba wuta (TCN) wanda wasu tsageru suka lalata, kwatsam bam ɗin ya tashi da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya mai tushe a cikin hukumar NSCDC reshen jihar Borno ta shaida wa Leadership cewa Nurudeen na taka wurin da aka ɗana bam ɗin, ya ankarar da abokan aikinsa su matsa.
Yana ɗaga kafarsa daga wurin nan take na'urar da aka dasa abun fashewar ta tashi, ta ji masa munanan raunukan da suka zama ajalinsa.
NSCDC ta tabbatar da faruwar lamarin
Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar NSCDC ta jihar, Bulus James, ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Jumu'a.
Ya bayyana cewa Nurudeen na kan aiki ne a cikin tawagar dakarun RRS, waɗanda ke cikin jami'an da suke sintiri a kan titin suka kula da layukan wutar.
Rundunar RRS da ta kunshi NSCDC da sauran hukumomin tsaro, an kafa ta ne domin samar da tsaro a titin Maiduguri zuwa Damaturu wanda ‘yan Boko Haram ke yawan kai hari.
Kakakin NSCDC ya ce bayan faruwar lamarin, jami'an tsaro suka ɗauke gawar Nurudeen zuwa asibitin kwararru na jihar, inda aka tabbatar da rai ya yi halinsa.
A cewarsa, tuni aka masa jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kamar yadda sahara Reporters ta ruwaito.
Yan bindiga sun kai hari Abuja da Neja
A wani rahoton kuma Yan bindiga sun kai hari garuruwa uku a birnin tarayya Abuja da jihar Neja da ke maƙotaka, sun kashe mutane huɗu.
Rahotanni sun nuna cewa yayin hare-haren a lokuta daban-daban, yan ta'addan sun yi garkuwa da wasu mutane 39.
Asali: Legit.ng