Maganar Aure Na Rawa Bayan Saurayi Ya Sa Budurwa Ta Girkawa Danginsa Su 70 Abinci, Gishiri Ya Zarce

Maganar Aure Na Rawa Bayan Saurayi Ya Sa Budurwa Ta Girkawa Danginsa Su 70 Abinci, Gishiri Ya Zarce

  • Wani mutum ya nuna bacin ransa a soshiyal midiya bayan budurwarsa da ke farfadowa daga rashin lafiya ta bar gidansa cikin fushi
  • A cewar mutumin, budurwar wacce yake son aura ta harzuka saboda an ce ta dafa wa yan uwansa mutum 70 abinci
  • Mutumin ya ce lamarin ya jefa yan uwansa a kokwanto kuma hakan na iya shafar soyayyarsu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani mutumi ya ba da labarin sakamakon ziyarar da ya kai yankin Badagry tare da matar da yake son aura domin ta hadu da danginsa.

Ya ba wani mai amfani da shafinsa na Twitter mai suna @dr_adetountanni labarin abun da ya faru da shi wanda shi kuma ya watsa sakonnin a dandalin na X.

Kara karanta wannan

Ba a gama da matsalar Kano ba, budurwa ta sake yin ajalin saurayinta magidanci, bayanai sun fito

Saurayi ya nemi budurwa ta dafawa danginsa 70 abinci
Matar jikin hoton bata da alaka da labarin Hoto: @Jorge Fernández, @dr_adetounanni/X app.
Asali: UGC

A cewarsa, ya yi tsammanin budurwar tasa za ta girkawa akalla danginsa mutum 70 ciki harda kanne da abokansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A al'adar gidansu dole ne ta tabbatar masu cewar ita din matar aure ce ta hanyar girka shinkafa da miyan alayyaho.

Ya ce an daukewa mai shirin zama matar tasa sakwara saboda rashin lafiyar da ta yi kwanan nan kuma tana kan farfadowa ne.

Sai dai kuma, bayan dandana abincin, sai mutumin ya ga cewa gishiri ya yi yawa inda ya nuna rashin jin dadinsa.

Da jin korafin mutumin cewa gishiri ya yi yawa a abincin, sai budurwar ta fusata sannan ta fara zaginsa.

Tashin hankalin ya yi yawa, wanda ya kai ta ga barin gidan a fusace. Mutumin ya yi hasashen cewa lamarin ya sa yan uwansa shakku a kanta, wanda hakan ka iya kawo tangarda ga soyayyarsu.

Kara karanta wannan

"Yadda mutum zai yi kudi bayan ya isa Canada": Matashi da ke zaune a Turai ya yi muhimmin bayani

Soyayyar wani mutum da budurwarsa ya shiga garari bayan ta girkawa danginsa su 70 abinci

Mutumin ya nuna damuwa cewa masoyiyar tasa ta bata kanta a wajen yan uwansa.

Yana ganin cewa lamarin na iya kawo tangarda wanda ba zai iya gyaruwa ba a soyayyarsu. Ya ce soyayyarsu ta samu tangarda ne a daidai lokacin da suke shirin yin baiko.

Jama'a sun yi martani

@Abigailsam18 ta yi martani:

"Ina fatan budurwar za ta ga wannan wallafar sannan ta guje ka. Iyali masu cike da mugunta."

@zhurg_ ta yi martani:

"Abincin mutum 70? Sauran mutum 69 din guragu ne?"

@OloriOfOloris ta yi martani:

"Kai da yan uwanka baku da tunani ko kadan."

Matashi ya ba abokinsa gudunmawar aure N3k

A wani labarin, mun ji cewa wani mutumi da ke zaune a Birtaniya ya bayar da gudunmawar N3,000 saboda bikin abokinsa da za a yi a Najeriya.

Wani abokinsu wanda ke a kungiyar WhatsApp da aka bude don karbar gudunmawar bikin ne ya ba da labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng